Mawakin dai ya cire faifan bidiyon wakar mai suna 'Jaye Lo' mai tsawon dakika 45, wanda ya nuna wasu maza sanye da fararen jellabiya da hula suna tikar rawa a kan shimfidar sallah.
Kasar Netherlands ta fara wasan rukunin E da yin nasara da ci 1-0 a kan kasar Portugal a gasar cin kofin duniya ta mata da aka buga a filin wasa na Dunedin a yau Lahadi, kuma Stefanie Van der Gragt ce ta ci kwallon kafin a tafi hutun rabin lokaci na wasan bayan bitar na’urar VAR.
Ana samun ciwon ne sakamakon doguwar nakuda yayin da da yake yunkurin fitowa, inda kuma mahaifiyar ba ta samun kulawar gaggawa da ta dace a asibiti.
Jami’ai a kasar Canada sun ce akalla mutane 15 su ka mutu a ranar Alhamis a lokacin da wata babbar motar daukar kaya ta yi karo da wata karamar motar safa da ke dauke da wasu mutane, galibi dattawa, a kan hanyarsu ta zuwa gidan caca a lardin Monitoba na kasar Canada.
Tsohon Firaministan Italiya wanda aka yi ta takaddama da shi, Silvio Berlusconi, ya mutu yana da shekaru 86 da haihuwa a duniya.
Gajiya, jiri, da rashin kiba wasu alamun rashin samun ingantaccen abinci mai gina jiki ne. Haka kuma kiba, rashin abinci mai gina jiki yana da alaka da rashin wadataccen abinci ko idan ya yiyawa, rashin daidaituwar abinci mai gina jiki, ko rashin ingancin abinci.
Wani mutum ya daba wa yara da manya biyu wuka a wani wurin shakatawa da safiyar ranar Alhamis, a wani hari da Macron ya ce ya girgiza kasar.
Domin Kari