A Ghana, wani yunkuri na fitar da tsarin biyan albashi ga matan shugaban kasa da na mataimakin shugaban kasa na haifar da ce-ce-ku-ce
Sudan ta Kudu ta cika shekara 10 da samun yanci kai yau Jumma’a sai dai babu wani abin kirki da za a yi murna a kasar da yakin basasa ya durkusar inda ake fama da rashin kwanciyar hankali na yau da kullum da kuma matsananciyar yunwa.
Lauyan shugaban kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB), Efeanyi Ejiofor, ya ce an azabtar da wanda ya ke karewa, Nnamdi Kanu yayin da ya ke a tsare a hannun hukumomin Kenya.
A Jamhuriyar Nijar masu sarrafa kayan noma da kiyo sun fara gudanar da taro domin tsayar da shawarwarin da za su gabatar a taron hukumar cimaka na birnin Roma da taron shekara shekara na Majalisar Dinkin Duniya da ke gudana a kowane watan Satumba a birnin New York.
UNICEF ta ce a ranar Alhamis din nan ta sanya hannu kan yarjejeniyar samar da allurar rigakafin COVID-19 ta Johnson & Johnson har miliyan 220 ga kasashe mambobin Tarayyar Afirka nan da karshen shekarar 2022.
Tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya mika kansa ga ‘yan sanda a safiyar yau Alhamis don fara zaman gidan yari na tsawon watanni 15.
Shugaban 'yan sandan kasar Haiti ya ce an kashe mutane hudu da ake zargi da kisan shugaba Jovenel Moise jiya Laraba a wata musayar wuta da ‘yan sanda.
A karshen zamanta na shekara shekara majalisar dokokin jamhuriyar Nijer ta shwaraci gwamnatin kasar ta kara jan damara domin kawo karshen aika-aikar ‘yan bindiga da ‘yan ta’addanda suka addabi jama’a.
Firai Ministan rikon kwarya Claude Joseph ya ce wasu 'yan bindiga sun kashe shugaban Haiti Jovenel Moïse.
Mahukuntan Najeriya da ke arewa maso yammacin jihar Kaduna sun rufe makarantu 13 bayan sace dalibai sama da 140 daga wata babbar makarantar Baptist ranar Litinin .
Jami’an Kamaru na zargin ‘yan tawaye daga Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da ketare iyaka da satar shanu da kuma sace mutanen gari don neman kudin fansa.
Masu garkuwa da mutane dauke da makamai sun sace dalibai 140 daga makarantar kwana da ke arewa maso yammacin Najeriya, kamar yadda jami’an yankin suka sanar a yauLitinin.
‘Yan bindiga sun yi garkuwa da kimanin mutane takwas, ciki har da dan wata ma’aikaciyar jinya mai shekara daya, daga gidajen ma’aikatan asibitin da ke zaune a arewa maso yammacin Najeriya.
A Ghana, 'yan adawa da wasu kungiyoyin farar hula na nuna damuwa kan yadda dimokradiyyar kasar ke kara tabarbarewa.
Al'umar Bingi cikin Karamar Hukumar Bungudu, a Jihar Zamfara dake arewacin Najeriya, sun datse hanyar Sokoto zuwa Zamfara don neman dauki daga gwamnati dangane da karuwar harin 'yan Bindiga a yankinsu.
Rundunar 'yan sandan jihar Borno ta kame wasu mutane goma da ake zargin aikata laifuka daban-daban da ya kama da na fashi, da zamba cikin aminci da kuma wasu da aka kama da tabar wiwi mai yawan gaske.
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta haramta amfani da mutum mutumi ga Masu shagunan sayar da kaya da teloli, inda ta ce yin haka ya sabawa addinin musulunci.
Shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum da gwamnan jihar Borno Farafesa Babagana Umara Zulum sun isa garin Diffa a da hantsin ranar Alhamis inda za su tattauna akan makomar ‘yan gudun hijira.
An sami kamfanin Donald Trump da kuma babban jami’i mai kula da harkokin kudinsa da laifukan da suka samo asali daga masu bincike na New York kan harkokin kasuwancin tsohon shugaban kasar.
Gwamnan Abdullahi Ganduje ya bukaci janye karar da ya shigar kan dan jarida Jaafar Jaafar, na badakalar bidiyon karbar dala da dan jaridar ya wallafa a shafinsa.
Domin Kari