Jami’an rundunar shiyyar Maiduguri na Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC, ta kama su a ranar Talata, 5 ga wannan watan na Maris.
Rahotanni daga Ngala hedkwatar Gambarou Ngala a jihar Borno, na cewa 'yan kungiyar Boko Haram sun yi garkuwa da kimanin mutane 319.
An gurfanar da wani fitaccen malami kuma mai fafutuka ‘dan kasar Sudan ta Kudu da ke gudun hijira a Amurka a jihar Arizona tare da wani dan kasar Utah da aka haifa a kasar Sudan ta Kudu bisa zargin saya da fitar da makamai na miliyoyin daloli domin kokarin kifar da gwamnatin kasarsu.
Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Aliko Dangote na shirin kafa wata kungiyar hada-hadar man fetur, mai yiwuwa a birnin Landan.
A Senegal ma matasa da suka kammala karatun jami’a suna fuskantar kalubale na rashin samun aikin yi da ya dace da fannin karatun da suka yi; Alkaluman kungiyar Statista, na nuna cewa bana, ana sa ran ma’aunin matsalar rashin aikin yi a nahiyar zai karu zuwa kashi bakwai cikin dari, da wasu rahotanni
Hukumar kare hakkin masu sayan kaya ta kasa (FCCPC), ta rufe katafaren kantin Sahad Store, a unguwar Garki dake birnin Abuja.
Nahiyar Afirka har yanzu na ci gaba da Fuskantar barazana daga Kungiyar masu tsattsauran ra'ayin addini ta IS yayin da ake fama da tashe-tashen hankula na siyasa a yammacin Afirka da yankin Sahel.
Domin Kari