Isra'ila ta fadawa wasu kasashen Turai hudu a yau Litinin cewa shirinsu na yin aiki don amincewa da kafa kasar Falasdinu ya zama "daukaka wa ta'addanci" wanda zai rage damar yin shawarwari na kawo karshen rikicin da ke tsakanin makwabtan.
Kungiyar agaji ta Red Crescent ta ce dakarun Isra'ila sun yi wa wasu asibitoci biyu kawanya a ranar Lahadin da ta gabata, inda suka yi ta luguden wuta kan jami'an kiwon lafiya, daga bisani Isra'ila ta ce ta kama 'yan ta'adda 480 yayin da aka ci gaba da gumurzu a babban asibitin Al Shifa na Gaza
Ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro (ONSA) ya tabbatar da tserewar manajan yankin Binance na Afirka, Nadeem Anjarwalla daga Najeriya.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta baiwa gwamnatin jihar Kano tallafin tireloli 100 na shinkafa, tirelolin dawa 44 da na masara guda hudu domin rabawa ga mabukata.
Wasu mutane hudu da ake zargi da kai harin a dakin raye-raye da wake-wake na kasar Rasha da ya kashe mutane sama da 130 sun gurfana a gaban kotu a birnin Moscow jiya Lahadi bisa zargin ta’addanci.
Biyo bayan umurnin shugaba Tinubu na gaggauta ceto daliban Kuriga sama da 280, babban hafsan tsaron Najeriya Janar Christopher Musa ya ce sojoji sun dukufa wajen ganin an ceto daliban da kuma hukunta ‘yan bindigan da ke wannan aika-aika, da wasu rahotanni
Domin Kari