A watan Yunin 2022, Shugaban Kasa Joe Biden ya gayyaci kusan kasashe 24 domin kaddamar da ayyanawar Los Angeles a kan kaura da bada kariya.
Daya daga cikin hanyoyin da mahukunta Rasha ke amfani dasu wajen uzzurawa rayuwar dimbin al'ummar Ukraine ita ce ta mayar da yanayin hunturu zuwa makami.
A yau Laraba, rundunar sojin Isra’ila ta bayyana cewar dakarun sojin kasanta dana motocin sulke zasu shiga cikin samamen da take kaiwa yankin kudancin Lebanon domin zafafa hare-haren da take kaiwa kungiyar Hizbullahi
A yau Talata, rundunar sojin Isra'ila ta gargadi al'ummomin dake zaune a yankunan kan iyakar Lebanon dasu kaurace daga kusan garuruwa 24 bayan da ta kaddamar da samamen da ta kira da kwarya-kwaryan kutse ta kasa akan mayakan kungiyar Hezbollah
A yau Litinin, fadar Kremlin ta yi Allah-wadai da kisan Shugaban Hizbullahi Hassan Nasrallah da hare-haren Isra’ila ta sama su ka yi a makon da ya gabata sannan tace tana da hasashe mai karfi dake nuna yiyuwar fadadar yaki a yankin Gabas ta Tsakiya.
Shugaban Hezbollah na riko ya sha alwashin ci gaba da yakar Isra’ila sannan ya bayyana cewar a shirye kungiyar take ta shafe dogon zango tana yaki duk kuwa da cewar an hallaka manyan kwamandojinta, ciki harda jagoranta, Hassan Nasrallah.
Gabanin fara bukukuwan murnar zagayowar ranar samun ‘yancin kan Najeriya karo na 64, rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayyar Najeriya tace ta tura wadatattun jami’ai da kayan aiki zuwa lungu da sako na garin Abuja.
Najeriya ta yi kira ga MDD da ta bayar da fifiko ga neman yafewa kasashe masu tasowa basussuka ta kuma bukaci a ba ta kujera ta dindindin a kwamitin tsaro na Majalisar; Mutanen da ambaliya ta lalatawa gidaje a Maiduguri suna zargin hukumomi da tashisu daga gine-ginen gwamnati, da wasu rahotanni
Domin Kari