Mai martaba Sarkin Shani Alhaji Nasiru Mohammadu Mailafiya ya ce yana tsoran sakin wasu masu garkuwa da mutane da jami'an tsaro suka kama.
Gwamnonin jahohi masu iyaka da Maradi ta jamhuruyar Nijar irin su Katsina da Zamfara da Sokoto da kuma Maradi sun gudanar da wata muhimmiyar ganawa a Maradi, inda suka tattauna game da matsalar tsaro da suke fama da ita a yankunan na su.
A ya yin da a yau al’ummar Musulmi a kasashen Duniya ke bukukuwan Sallar Ashura ta 10 ga watan Muharram, mabiya mazabar shi’ah a jamhuriyar Nijar sun yi muzahara.
Masana sun fara tofa albarkacin bakinsu a game da rasuwar tsohon shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe, wanda Allah ya yiwa cikawa a jiya bayan ya yi fama da rashin lafiya.
Tsawon makonni biyu kenan da kasar Nigeriya ta rufe iyakarta da Nijar, ba tare da tayi bayanin dalilan yin hakan ba.
Bayan kwana biyu da gwamnatin Najeriya ta rufe iyakokin kasar da wasu kasashe makwafta, ‘yan Najeriya mazauna jamhuriyar Nijar sun koka akan abinda suka kira cikas.
Hukumar yaki da cin hanci ta Najeriya a shiyyar Benin, tare da hada kai da abokan ta'annatin ta da ke Amurka, ta ce ta kama wata mata mai damfara ta yanar gizo.
Wasu mahara sun kai hari
Bankin raya masana’antun Najeriya ya nuna rashin amincewa da bukatar masu gasa burodin rogo, ya yafe bashin da su ka karba na Naira biliyan 3.4 don bunkasa wannan sana’a.
Gamayyar jam’iyun adawa na FRDDR ta fara yunkurin maka dan takarar jam’iyar PNDS Bazoum Mohamed mai mukamin ministan cikin gida a kotu saboda zarginsa da amfani da kadarori da ma’aikatan gwamnati.
Shirin mu na matasa da siyasa na wannan mako ya samu bakuncin Injiniya Rufa’I Dagumawa wakili a kungiyar Arewa Youth Assembly Gammayar, kungiyoyin matasan Arewacin Najeriya.
Wata kungiyar matasa a jamhuriyar Nijar, tare da hadin guiwar cibiyar raya al’adun Amurka, sun shirya wata mahawarar bainar jama’a da nufin fadakar da matasa illolin dake tattare da tsatsauran ra’ayin addini.
A Najeriya wani lauya dan kabilar Ibo ya nemi wata kotun tarraiya da ke Abuja, ta tilasta wa kasar Ingila ta yi maza ta dawo da shugaban haramtacciyar Kungiyar IPOB Nnamdi Kanu zuwa Najeriya domin ya fuskanci shari'a.
A shirin mu na mata da sana'a yau Dandalin VOA ya dira jihar Kaduna, inda wakiliyar Dandalin VOA Baraka Bashir, tayi hira da Zainab Lawal Nasarawa, mai sana’a Mocktail, wato samar da lemo ta hanyar sarrafa kayan marmari.
A lokacin da aka bude taron rundunar 'yan sandan Duniya wato INTERPOL, a Abuja, jami'an tsaron sun tattauna batun 'yan Najeriyan nan 77 da aka samu da hannu a wajen damfarar makudan kudade a Amurka.
Ma'aikatan Muryar Amurka sun ziyarci jami’ar garin Norfolk wato Norfolk State University inda aka kaddamar da taron shirye shiryen bukin tuna fataucin bayi.
Jam’iyun hamayya a jamhuriyar Nijar sun aika wa kungiyar ECOWAS wasika domin ta tsoma baki a rikicin da ya ki karewa, tsakanin bangarorin siyasar kasar, game da tsare tsaren zabukan da ake saran gudanarwa a shekarar 2020 da 2021.
Domin Kari