VOA60 AFIRKA: A takaitattun labaran Afirka na yau, a Najeriya gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya yi kiran azauna lafiya bayan da sojoji suka yi harbi kan masu zanga-zanga a unguwar Lekki da ke jihar Legas a yammacin Talata, rundunar sojojin ta karyata rahotannin, da wasu sauran labarai.
VOA60 DUNIYA: A takaitattun labaran duniya na yau, wata kotu a Thailand ta bada umarnin dakatar da wani gidan talabujin bayan gwamnati ta zargi tashar da saba matakan kawo karshen zanga-zanga ta tsawon watanni uku, da wasu sauran labarai.
VOA60 AFIRKA: A takaitattun labaran Afirka na yau, a Guinea babban jagoran 'yan adawa Cellou Dalein Diallo ya ce shi ne ya lashe zaben shugaban kasar, da wasu sauran labarai.
Dubun-dubatar ‘yan kasar ta Chile sun taru a tsakiyar dandalin na Santiago domin bikin tunawa da shekara guda na babbar zanga-zangar da ta yi sanadin mutuwar sama da 30 da kuma jikkata dubbai. Zanga-zangar ta rikici yayin da aka kona coci guda biyu kuma 'yan sanda suka harba hayaki mai sa hawaye.
VOA60 DUNIYA: A Bolivia, Luis Arce mai ra’ayin gurguzu ya kama hanyar lashe zaben shugabancin kasar ba tare da anje zagaye na biyu ba. Kawo yanzu ya samu fiye da kashi 52 na kuri’un da aka kada, da wasu sauran labarai.
VOA60 AFIRKA: Firayim Ministan Guinea Ibrahima Kassory Fofana ya ce an kada kuri'a a zaben shugaban kasa na ranar Lahadi ba tare da wani rikici ba. Ya bukaci dukkan bangarorin da kada sanar da sakamakon kafin hukumar zaben ta yi hakan, da wasu sauran labarai.
A Daina Shan Kwaya: A ci gaba da hira da Kungiyoyin Young Ambassadors da na Northern Nigerian Women Initiative, za mu ji mene ne burinsu, me suke bukata daga Al’umma, kuma me Al’umma ke bukata daga gwamnatin kasar don shawo kan wannan illar ta shaye-shayen miyagun kwayoyi.
TASKAR VOA: Yayin da ake fama da tsadar kayan abinci a Najeriya ‘yan kasar da yawa na ci gaba da yin kira ga gwamnati da ta dauki matakan shawo kan hauhawar farashin kayan masarufi a kasar, da wasu sauran rahotanni.
LAFIYARMU: Yadda cin zarafin iyali ke karuwa a fadin duniya, da kuma adinda kwararru da bincike ke nuna wa, da wasu sauran rahotanni
VOA60 DUNIYA: A takaitattun labaran Duniya na yau,'yan sanda a Thailand sun harba wani ruwa mai zafi kan dubban masu zanga zangar adawa da gwamnatin Firai minsta Prayuth Chan-ochan wacce ta rikide zuwa tashin hankali, da wasu sauran labarai.
#VOA60 AFIRKA: A takaitattun labaran Afirka na yau, a Guinea magoya bayan jam’iyyar adawa ta UFDG sun tarbi dan takararsu, Cellou Dalein Diallo, a babban birnin kasar Conakry, a ranar karshe ta kamfe kafin zaben ranar Lahadi, da wasu sauran labarai.
Ga jerin ‘yan wasan kwallon kafa da manajoji wadanda suka kamu da cutar Coronavirus.
Zanga-zangar adawa da cin zarafin da ‘yan sanda ke yiwa jama’a a Najeriya ta ci gaba da gudana a kasar har tsawon mako guda yayin da masu zanga-zangar suka yi ta mamaye titunan manyan biranen kasar, suna hana zirga-zirga tare da tsayar da harkokin kasuwanci.
Ruwan sama kamar da bakin kwarya da ambaliyar ruwa a kudancin Telangana da ke kudancin Indiya sun rusa gidaje kuma suka kashe akalla mutane 15, in ji ‘yan sanda
VOA60 DUNIYA: A takaitattun labaran duniya na yau, a Belgium hukumar Tarayyar Turai ta bukaci kasashe membobin kungiyar da su kara kaimi don dakile karuwar cutar Coronavirus, ta kuma ba da shawarar daukar matakai na fitar da allurar rigakafin, da wasu sauran labarai.
VOA60 AFIRKA: A takaitattun labaran Afirka na yau, 'yan kasar Guinea za su yi zabe ranar Lahadi inda shugaba Alpha Conde, mai yawan shekaru ke neman tsawaita mulkinsa, abinda ya janyo mashi kakkausar suka daga abokan hamayya, da wasu sauran labarai.
'Yan kwana-kwana a Tanzania na ci gaba da kokarin shawo kan gobara a Dutsen Kilimanjaro, tsauni mafi tsayi a Afirka.Ya ɓarke ne a ranar Lahadi, 11 ga Oktoba. Wani jami’i daga hukumar kula da gandun daji ya ce wutar tana ci gaba da ci.
VOA60 DUNIYA: Dubban masu zanga-zangar kin jinin gwamnati a Thailand, sun mamaye wani gini mai tarihi ga dimukradiya a Bangkok, bayan sun yi arangama da masu goyon bayan tsarin masarauta, da wasu sauran labarai.
VOA60 AFIRKA: : Dan takarar shugaban kasa a Guinea, Cellou Dalein Diallo, kuma shugaban babbar jam'iyyar adawa, ya ce, magoya bayan Shugaba Alpha Condé sun hana tawagarsa shiga birni Kankan don yakin neman zabe, wasu sauran labarai.,
Domin Kari