LAFIYARMU: Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce an fara samun karuwar masu kamuwa da cutar COVID-19 tun daga farkon watan Oktoba a kalla a kasashe 20 na Nahiyar Afirka sakamakon tarukan jama'a da kuma tafiye-tafiye, da wasu sauran labarai.
A cikin shirin Taska na wannan makon, kwamitocin bincike da gwamnatoci suka kafa game da zarge-zargen cin zarafin jama’a da ake yiwa ‘yan sanda a Najeriya, suna ci gaba da karban koken jama’a, da wasu sauran labarai.
VOA60 DUNIYA: A takaitatun labaran duniya na yau Shugaba Donald Trump ya ce zai bar fadar White House idan kuri'un kwaleji da za a tabbatar 14 ga watan Disamba suka tabbatar da Joe Biden a matsayin wanda ya yi nasara, da wasu sauran labarai
VOA60 DUNIYA: A takaitattun labaran duniya na yau 'yan gudun hijira daga yankin Tigray na Habasha sun ce sun ga ana kashe mutane akan titi sannan sun ji karar harbe-harbe, Habasha ta bayyana rikicin a matsayin matakin tabbatar da doka a kasar, da wasu sauran labarai.
VOA60 AFIRKA: A takaitattun labaran Afirka na yau wata kungiyar matasa a garin Mai Kadra a Ethiopia tare da taimakon 'yan sanda da wata kungiyar 'yan bindiga ta kashe a kalla mutane 600 a ranar 9 ga watan Nuwamban nan a yankin Tigray, da wasu sauran labarai.
VOA60 DUNIYA: A takaitattun labaran duniya na yau China ta harba kumbo zuwa duniyar wata da nufin dauko duwatsu daga duniyar wanda shi ne karo na farko da wata kasa a duniya tayi yunkurin samo samfurin duniyar watan tun 1970, da wasu sauran labarai.
VOA60 AFIRKA: A takaitattun labaran Afirka na yau gwamnatin Habasha ta na sake gargadin mutane da suke zagaye da babban birnin yankin Tigray da su bar wurin, da wasu sauran labarai.
VOA60 DUNIYA: A takaitattiun labaran duniya na yau tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy ya isa kotu a Paris domin fuskantar tuhume-tuhumen cin hanci da rashawa, da wasu sauran labarai.
VOA60 AFIRKA: A takaitattiun labaran Afirka na yau rundunar sojin Habasha ta na gargadin fararen hula da suka kewaye baban birnin Tigray cewa muddin basu gudu ba to ba sani ba sabo, da wasu sauran labarai.
A Cikin shirin mu na wannan makon wanda zai zamana kashi na uku za mu ci gaba da hira da wakilin Muryar Amurka Mahmud Ibrahim Kwari da ke Kano a Najeriya da chairman na NDLEA Muhammad Mustapha Abdullah akan irin fadi-tashin da suke yi na hana shigar miyagun kwayoyi cikin kasar da kuma burin sa.
An gano kasusuwan abin da ake zaton wani attajiri ne da bawansa da ke tserewa daga dutse mai aman wuta na Vesuvius kusan shekaru 2,000 da suka gabata a Pompeii, in ji jami'ai a wurin shakatawa na kayan tarihi.
LAFIYARMU: A cikin shirin wannan makon ciwon suga wani mugun ciwo ne dake sa sinadarin da ke cikin jini ya yi yawa fiye da kima, ga shawarar da Hukmumar Lafiya ta Duniya ta bayar da kuma abinda wasu masu dauke da cutar ke cewa daga Najeriya.
A cikin shirin TASKA na wannan makon an samu gagarumar nasara a yunkurin samar da maganin riga kafin cutar coronavirus a Amurka. Sai dai kuma ana fargabar cewa wasu kasashen ba su da kwarewa wajen kulawa da riga kafin, da wasu sauran labarai
Kwamitin karkashin shugabancin Mai Martaba Sarkin Lafiya, Mai Shari’a, Sidi Muhammad zai duba hanyoyin da sarakuna zasu shiga a dama dasu cikin harkokin mulki, musamman a shiyyar Arewacin Najeriya
VOA60 DUNIYA: A takaitattiun labaran duniya na yau Japan ta daga matakan ta baci na coronavirus zuwa makura bayan yawan sabbin masu kamuwa da cutar a rana ya haura 600, da wasu sauran labarai
VOA60 AFIRKA: A takaitattun labaran Afirka na yau jam'iyya mai mulki a yankin Tigray na Habasha ta harba makaman roka zuwa Asmara babban birnin Eritrea, da wasu sauran labarai.
VOA60 DUNIYA: A takaitattun labaran duniya na yau yawan mutanen da coronavirus ta kashe a Amurka ya haura duba dari biyu da hamsin yayin da ake samun karuwar masu cutar a fadin kasar, da wasu sauran labarai.
VOA60 AFIRKA: A takaitattun labaran Afirka na yau rundunar sojin Habasha ta zargi shugabar Hukumar Lafiya ta Duniya da kokarin samar da makamai da kuma taimako na diflomasiya ga babbar jami'iyya a Tigray wacce ka fada da sojojin gwamnati, da wasu sauran labarai.
Domin Kari