A cikin shirin TASKA na wannan makon daga jamhuriyar Nijar ga yadda ta kaya a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin kasar da aka gudana a ranar 27 ga watan Disamba 2020, Sannan hukumomin jihar Borno a Najeriya na kokarin fito da wani shiri na kare manoma, da wasu sauran rahotanni.
LAFIYARMU: Kwararru sun ce akwai wasu illoli ko matsaloli da COVID-19 ke iya haifarwa na tsawon watanni ga wadanda suka warke daga cutar, da wasu sauran rahotanni.
Masu tausar suna amfani da nau'ika 28 daban-daban na macizai marasa haɗari a cikin kowane zaman tausa na minti 30. Mai gidan shakatawar, Safwan Sedki, ya ce an tabbatar da cewa tausa jiki da maciji na rage radadin ciwo da inganta haɓakar jini a cikin jiki. - Reuters
VOA60 DUNIYA: A Takaitattun labaran duniya na yau shugaba Donald Trump ya sanya hannu akan shirin tallafawa jama'a na annobar Coronavirus na dala biliyan 900 bayan a farko ya ki amincewa da yarjejeniyar, da wasu sauran labarai.
VOA60 AFIRKA: A takaitattun labaran Afirka na yau kungiyar Boko Haram ta kasahe a kalla mutane goma da jami'an tsaro hudu yayin wani hari a kauyuka uku a Arewa maso gabashin Najeriy, da wasu sauran labarai.
Shugaban da ya ki ya sanya hannu a kudurin tallafin, ya na mai cewa ya so a ba Amurkawa dala 2,000.
An yankewa wata ‘yar jarida ‘yar kasar China hukuncin zuwa gidan yari tsawon shekara 4 saboda yadda ta bada rahotanni kai-tsaye daga Wuhan a lokacin da aka samu bullar annobar COVID-19.
A cikin shirin mu na wannan makon wakilin Muryar Amurka daga Abuja a Najeriya Nasiru Adamu El-Hikaya zai ci gaba da tattaunawa da Mukhtar Iliya Imedi shugaban kungiyar Initiative For The Fight Against Drug Abusa & Enlightenment akan wasu kayan gargajiya da ake amfani da su wajen maye: Kashi Na Biyu
Hukumar zabe ta CENI a Jamhuriyar Nijar, ta ce ana gudanar da zabe a yau Litinin 28 ga watan Disamba a yankin Madama da ke jihar Agadez.
Ofishin jakadancin Amurka da ke Yamai, babban birnin Nijar, ya yaba da yadda aka gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki cikin lumana.
A cikin shirin wannan makon, jama’a a Najeriya na ci gaba da magana kan bukatar kare makarantu, bayan satar dalibai sama da 300 da aka yi a jihar Katsina, da wasu sauran rahotanni.
VOA60 DUNIYA: A takaitattun labaran duniya na yau wani bidiyo da aka fitar ya nuna lokacin da wani 'dan sanda wanda ya tashi daga aiki ya harbe wata mata da 'danta a Philippines abin da ya sa mutane ka ta Allah wadai da al'amarin, da wasu sauran labarai.
VOA60 AFIRKA: A takaitattun labaran Afirka na yau shugaban Jamhuriyar Tsakiyar Afirka ya yi kira ga mutane da su fito su kada kuri'a a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki, da wasu sauran labarai.
A cikin shirin mu na wannan makon wakilin Muryar Amurka daga Abuja a Najeriya Nasiru Adamu El-Hikaya ya aiko mana da hirarsu da Mukhtar Iliya Imedi shugaban kungiyar Initiative For The Fight Against Drug Abusa & Enlightenment dake fadakar da jama’a akan illolin miyagun kwayoyi-Kashi Na Farko
'Yan Najeriya na ci gaba da kokawa game da matsalar tsaro a kasar musamman ma batun harin da 'yan bindiga suka kai kwanan nan a wata makantar kwana da ke garin Kankara a jihar Katsina.
Yayinda kamfanoni ke tsere don ƙirƙirar rigakafin COVID-19 da ƙasashe ke warwason tabbatar da samu, wasu tambayoyi sun bullo game da amfani da kayayyakin alade a yin rigakafin.
Likitoci a Kenya da ke aiki a asibitocin gwamnati sun fara yajin aikin gama gari ranar Litinin 21 ga watan Disamba akan rashin Insura mai kyau da kuma kayan kariya a yayin da su ke jinyar masu cutar COVID-19, a cewar kungiyar jami’an lafiyar.
Matakan bada tallafin sun hada da taimaka wa masana'antu don ma'aikatansu su ci gaba da aiki, da kuma ba Amurkawa tallafin kudi na kai tsaye.
Hukumar kula da hakkoki da karfafa gwiwar ‘yan kasa akan harkokin albarkatun mai da Iskar gas ta Najeriya ta ce damar da kamfanonin cikin gida masu hada-hada a bangaren albarkatun mai na kasar sun karu da kimanin kashi 30 cikin dari.
A cikin shirin Taska na wannan makon an fara raba maganin Pfizer da BioNTech na coronavirus a Amurka, abin da ya bayar da damar fara yiwa Amurkawa rigakafin cutar cikin ‘yan kwanaki, da wasu sauran rahotanni.
Domin Kari