Mata a jihar Plato sun jaddada bukatar cika alkawarin da aka dauka na basu kashi talatin cikin dari na makaman siyasa, yayin da su ke bukin ranar mata ta duniya.
A cikin shirin na wannan makon, a Najeriya, matsalar sace dalibai daga makarantunsu da ake ci gaba da samu ta na neman kassara sha’anin ilimi a Arewacin kasar, da wasu sauran rahotanni.
Gwamnatin jihar Nejan Najeriya ta sanar da rasuwar Sarkin Kagara mai daraja ta daya mai martaba Alhaji Salihu Tanko da yammacin ranar Talata.
Gwamnatin Nigeria ta ba da umurnin hana hakar zinari da sauran albarkatun ‘kasa a jihar Zamfara tare da haramta shawagin jiragen sama a sararin samaniyar jihar A kokarin yaki da ta’ adds ci ya yayi kamari a jihar.
Gwamnatin jihar Kano ta ce shirinta na zamanantar da tsarin karatun tsangayu a jihar na ci gaba da samun nasara, duk kuwa da dinbin kalubale.
Wasu cikin mata da ke karkashin Gamayyar Kungiyoyin Mata ta Najeriya a karkashin jagorancin Madam Gloria Laraba Shoda sun yi kira ga Gwamnati da ta karfafa hukumomni tsaro don magance yawan sace sacen dalibai da ake yi a makarantu.
Jamhuriyar Benin tana shirin kulla kawance da Najeriya a haujin noman shinkafa domin habbaka samarwa da dogaro da shinkafar da suka noma cikin gida ga kasashen biyu.
Babban kamfanin man fetur na Najeriya wato NNPC ya janye batun kara farashi a kan kowacce litar mai da ya shirya yi daga ranar 1 ga watan Maris, bayan zama da masu ruwa da tsaki a fannin albarkatun man fetur din.
An fara samun kwanciyar hankali bayan wata hatsaniya da ta barke tsakanin daliban jami'ar kimiya ta kere kere ta jihar Kebbi dake Aliero da kuma mutanen garin.
Hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi ta kaddamar da bincike akan wani mutum da aka kama da hodar cocaine da aka kiyasta kudinta ya kai naira biliyan daya.
Sannan a jihar Bornon Najeriya, hukumomi sun tashi tsaye wajen gyara wata na’urar lantarki da mayakan Boko Haram suka lalata, abin da ya jefa dubban mutane cikin duhu sama da makonni uku, da wasu sauran rahotanni.
A Najeriya matsalar rashin tsaro na ci gaba da ta'azzara; abin da yasa al'ummomi ke ta yin kaura daga garuruwansu domin neman tsira, kamar yadda yake faruwa a jihar Kebbi da ke Arewacin kasar.
A karon farko kasar Ghana ta karbi alluran rigakafin coronavirus da ake samarwa ta hanyar shirin raba alluran rigakafi na bai daya a duniya da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ke kula da shi.
Sababbin shugabanin hukumomin tsaro da Majalisar Dattawa Najeriya ta tantance sun yi alkawarin za a samu sauki a matsalar tsaro da ke addabar Kasar nan ba da jimawa ba.
Da yammacin jiya da misalin karfe shida na maraice ne mazauna birnin Maiduguri suka fara jin karar wasu ababe masu fashewa kamar bam.
Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta ce ta amince da yi sulhu da ‘yan bindiga idan har hakan zai taimaka wajen magance matsalar hare haren ‘yan bidigar da suka addabi musamman yankin Arewacin kasar.
Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya kyankyasa inda yake ganin masu garkuwa da mutane suka boye daliban makarantar Kwalejin Kimiyya ta Kagara da ke jihar Neja.
A Jamhuriyar Nijar, an shiga jimamin mutuwar ma'aikatan zabe da suka rasa rayukansu bayan da motarsu ta taka nakiya a yankin Tillabery.
Sannan masu sharhi kan harkokin yau da kullun a Najeriya na ci gaba da tsokaci a game da irin aikin dake gaban sabbin manyan hafsoshin tsaron kasar da suka kama aiki kwanan nan, da wasu sauran rahotanni.
Domin Kari