Kasar Isra’ila da kungiyar Hezbullah mai samun goyon bayan Iran na daf da kulla yarjejeniyar tsagaita wuta a yau Talata, abinda zai share hanyar kawo karshen rikicin da ya yi sanadiyar salwantar rayukan dubban jama’a tun bayan da yakin Gaza ya tayar da shi watanni 14 da suka gabata
Annobar COVID ta sauya duniya, a cewar sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, a jawabin daya gabatar a taron bunkasa tattalin arzikin kasashen Asiya da Pacific (APEC), na shekara-shekara dake gudana a birnin Lima, na kasar Peru.
Zababben shugaban Amurka Donald Trump ya nuna burinsa na cika alkawura ga shugabannin kasashe na gaggauta kawo karshen tashe-tashen hankali a Gabas ta Tsakiya da Ukraine; Ministan abinci da noma a Ghana ya kaddamar da wani sabon shirin karfafawa manoma gwiwa don bunkasa noma, da wasu rahotanni
Kasar Rasha ta harba makamai masu linzami masu cin dogon zango zuwa birnin Dnipro na Ukraine a yau Alhamis, a cewar rundunar mayakan saman birnin Kyiv, a wani al’amari da za’a iya kira da karon farko na yin amafani da makaman da aka kera domin kai harin nukiliya zuwa nesa.
An yi garkuwa da wani fitaccen 'dan siyasar Uganda Kizza Besigye, bangaren adawa yayin bikin kaddamar da littafi a kasar Kenya a karshen makon daya gabata
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya amince da tattaunawa kan batun tsagaita wuta a yakin Ukraine tsakaninsa da Donald Trump sai dai ya ce ba zai mayarwa Ukraine yankunanta daya mamaye ba.
Domin Kari