Wasu ‘yan siyasa daga Arewaci da Kudancin Najeriya sun kafa gwamnati ko kungiyar sa ido kan ayyukan gwamnati mai ci da su ke zayyanawa da cewa ta gaza.
A Najeriya yawan hare hare da kissan kiyashi da ake yi wa ‘yan kasar na ci gaba da tunzura jama'a har sun fara tunanin daukarwa kan su mataki sabodagwamnati ta fita batun su.
Hadin gwiwar sojojin jamhuriyar Nijar da takwarorinsu na Burkina Faso sun yi nasarar wargaza wani sansanin 'yan ta'adda dake kan iyakar kasashen biyu, lamarin da ya ba su damar kashe 'yan ta'adda kusan 100 tare da kama makamai da babura fiye da 200.
Hukumomin jamhuriyar Nijar sun kama shugaban kungiyar hadin kan al’umar jihar Tilabery Amadou Harouna Maiga bayan da ya yi wasu kalamai dangane da zanga-zangar nan ta matasan da suka datsewa ayarin motocin sojan Faransa hanya a garin Tera a ranar 27 ga watan November 2021.
Cibiyar ba da lasisin kwarewa kan ayyukan kwangiloli ta Najeriya “Chartered institute” ta ce za ta fara daukar matakan gurfanar da wadanda ba su da lasisi a jami’an da kan gudanar da ayyukan kwangiloli don yaki da baragurbi.
Gwamantin Amurka ta bai wa jamhuriyar Nijer gudummuwar jirgin sama samfarin Hercules C 130 domin amfanin sojojin kasar a yakin da suke kafsawa da 'yan ta'adda.
A Najeriya kungiyoyi da hukumomi da ke fafatukar kare hakkokin bil'adama na ci gaba da daura damarar ceto rayukan jama'a musamman kananan yara da kan iya fadawa tarkon cin zarafi.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kara jaddada kudirin gwamnatinsa na wadata mayakan kasar da isassu kuma ingatattun kayan aiki don ci gaba da tunkarar matsalolin tsaro dake addabar kasar a sassa daban-daban.
Shugabannin al’umma a Jamhuriyar Nijar sun bukaci gudunmawa daga kungiyoyi masu zaman kansu wajen samar da ayyukan yi a karkara irinsu noman rani da nufin cire wa matasa tunanin zuwa kasashen waje.
Hukumomim jamhuriyar Nijar sun tabbatar da mutuwar sojojin kasar 12 sakamakon harin da aka kai a kauyen Fantio na gundumar Tera a shekaran jiya asabar yayinda sojojin suka kashe gomman ‘yan ta’adda suka kuma kwace babura da dama da na’urorin sadarwa.
A cikin shirin na wannan makon ‘yan Najeriya na ci gaba da mayar da martani ga yunkurin gwamnantin kasar na cire tallafin mai a shekara mai kamawa, da wasu rahotanni
Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Shugaban kasa Cyril Ramaphosa sun kaddamar da taron tattaunawa tsakanin matasan Najeriya da Afirka ta Kudu ranar Alhamis a Abuja, don samar da zaman lafiya da tsaro, ci gaban matasa da kuma shiga harkokin siyasa.
A jamhuriyar Nijar masu shagunan kemis kemis wato pharmacie sun dakatar da aiki daga yau Laraba 1 ga watan Disamba har sai yadda hali ya yi.
Tawagogin matasa daga kasashen G5 Sahel sun hallara a jamhuriyar Nijar don tattauna hanyoyin kafa wata majalisar matasan kasashen wannan yanki a ci gaba da neman hanyoyin kare matasa daga tarkon ‘yan ta’adda a wannan lokaci na yawaitar aika-aikar ‘yan bindiga.
A cikin shirin na wannan makon wasu mazauna kauyukan jihar Sokoto a Najeriya sun yi wa Muryar Amurka karin haske game da karbe iko a garuruwansu da 'yan bindiga suka yi, da wasu rahotanni
A cikin shirin na wannan makon a Jamhuriyar Nijar Sashin Hausa na Muryar Amurka ya shirya wani taro na tattauna matsalar tsaro da ake fuskanta, inda masu sharhi kan al’amura a kasar da dama suka halarci taron, da wasu rahotanni
Domin Kari