Rundunar sojan Ruwa ta Najeriya, ta sanar cewar ta kama wasu jiragen ruwa goma sha biyu, dake dakon mai da aka sato a yankin Neja Dalta a wani samamen hadin gwiwa da ta kaddamar a yakin mai suna Operation Dakatar da Barawo.
Hukumomin kasar Kamaru sun tabbatar da wata rundunar tsaro ta musamman ta ceto wasu yara daga hannun masu garkuwa da mutanen domin samun kudin fansa bayan wata musayar wuta tsakanin jami’an tsaron a garin Mayo Rey da ya yi sanadiyar raunata mutum guda a cikin masu garkuwan.
Farautar mutumin da ya kai harin kan mai-uwa-da-wabi da safiyar yau Talata a gundumar Brooklyn ta birnin New York ta hadu da tsaiko yau da rana yayin da aka gano kyamarar daukar hoto a tashar jirgin kasa na layin 36th street da ya kamata ta dau hoton maharin ta lalace.
Matasan bakar fatar Afurka suna kaurin suna wurin aikata kaifuka a birnin New York a cewar jami’an tsaron birnin.
Yayin da hankalin duniya ya karkata a kan yaki tsakanin kasashen Rasha da Ukraine, birnin New York a Amurka na daukar matakan kare al’ummarsa daga barazanar da cutar coronavirus ke yi a birnin da ya taba zama tungar annobar COVID-19 duniya.
Mazauna jihar New York sun gudanar da zanga zangar kin jinin harin da Rasha ta kai a kan Ukraine, yayin da shugaban Amurka Joe Biden ya sanar da sabbin takunkumai a kan Rasha.
Ƙungiyar CAF ta dau matakai bayan hadari da ya afku a filin wasan ƙwallon ƙafa na Olembe a Yaoundé. Inda mutun 8 suka rasa rayukan su, sama da 30 kuma suka jikkata.
Bayanai sun yi nuni da cewa a lokacin da hatsarin ya faru direban ya sauka daga motar yana yekuwar mutane sun gudu daga wurin.
Daruruwan mutane daga sassa daban na gudandumar Bronx da ma New York da suka hada da Musulmi ne suka halarci sallar jana’iza.
Shahararren dan wasan gaba na Liverpool Salah bai tabuka abin kirki ba, sakamakon yadda zaratan ‘yan wasan Najeriya suka rike shi tsawon mintuna 90 da aka yi a wasan.
Kididdiga ta nuna cewa, kimanin mutum 44 ne suka ji rauni inda 13 daga cikinsu ke cikin mawuyacin hali.
Wani bam da ya tashi a jiya Lahadi da rana a wajen babban masallacin birnin Kabul ya kashe akalla fararen hula biyar kana ya jikata akalla wasu mutane hudu, inji Qari Saeed Khosti, kakakin ma’aikatar harkokin cikin gida na Taliban.
Kungiyar Boko Haram ta kwace kauyuka da dama a jihar Neja dake arewa maso tsakiyar Najeriya, suna baiwa mutanen kauyukan kudin suna saka su yaki da gwamnati, a cewar wani jami’in karamar hukuma da hukumar yada labaran jihar, suna fadawa Reuters
A ranar Talatar makon jiya ne shugabannin kasashe da shugabannin gwamnatoci suka fara jawabai a mahawarar babban taron kolin Majalisar Dinkin Duniya na cikon shekaru 76 a birnin New York.
Kamar yadda aka zata tun farko, jawaban Shugabannin na Afurka sun fi raja'a ne ga batun annobar COVID-19, matsalolin tsaro da kuma na tattalin arziki.
Wata zanga-zangar nuna damuwa akan kara tabarbarewar sha'anin tsaro a garin Isa da ke jihar Sokoto, ta rikide zuwa tarzoma, lamarin da ya yi sanadiyyar kai farmaki tare da kona gidajen kwamishinan lamurran tsaro da kuma na basaraken garin na Isa.
Shugabannin kasashen Afurka da dama ne suka yi jawabansu a rana ta biyu a taron kolin na Majalisar Dinkin Duniya. Sai dai bayanan shugabannin sun fi maida hankali ne a kan batun coronavirus da batun raba rigakafin annobar daidai tsakanin kasashe.
Rundunar hadin gwiwar G5 Sahel ta sanar da samun nasarar kama wasu ‘yan ta’adda sama da 10 a yankin iyakokin kasashen Nijer, Burkina, Faso da Mali bayan da ta bi diddigin wasu bayanan da ta samu daga al’ummar kauyukan jihar Tilabery.
Domin Kari