Mataimakiyar shugaban kasar Amurka Kamala Haris ta gana da shugaban kasar Ghana Nana Akuffo Addo a fadar shugabancin kasar inda suka tattauna akan wasu muhimman batutuwan da suka hada da tsaro da tattalin arziki da dai sauransu.
Shugaban adawa na kasar Kenya Raila Odinga ya yi kira ga al'ummar kasar su fita su gudanar zanga zangar kin jinin gwamnati bisa tsadar rayuwa.
Gwamnatin Burkina Faso dake karkashin mulkin soja ta dakatar da kafar yada labarai ta France 24 a kasar bayan da ta yada wata hirar da tayi da shugaban Al-Qaida na yankin arewacin Afika AQIM.
An fara samun nasarar ayyukan tsaro na hadin gwiwa tsakanin kasashen Mali da Nijar masu fama da matsalar rashin tsaro.
Daukan wannan mataki na zuwa ne yayin da ya rage 'yan kwanaki a gudanar da zaben gwamnoni da na 'yan majalisun jihohi a wasu jihohin kasar.
A ranar Larabar da ta gabata ne wata kotun Magistira a Kano ta tisa keyar shugaban masu rinjayen na majalisar tarayya zuwa gidan gyara hali.
A ranar Litinin wasu daga cikin wakilan jam'iyyun na bangaren 'yan adawa suka fice daga zauren tattara sakamakon zaben bayan da suka nuna rashin gamsuwar kan abin da ke faruwa.
Yayin da ake ci gaba da murnar shirin fara hako mai a arewacin Najeriya, za kuma a saurari abubuwan da 'yan rajin kare muhalli za su ce, a kalla nan gaba.
Domin Kari