A Nijar, Jami'ai sun ce akalla bakin haure 250 daga kasashe da suka hada da Najeriya, da Ghana, da Burkina Faso suna jiran a yi jigilar su zuwa birnin Agadez na kasar inda za’a kebe su na kwanaki 14 bayan masu fasakwauri sun watsar da su.
A Somaliya kuwa, wasu mata ne suka ce Coronavirus ta haifar musu da wani cigaba da basu yi tsammani ba, tun bayan hana saukar jiragen kasa-da-kasa da aka yi.Wanda ya hada da jirgin da ke kawo ganyen Khat daga makociyar su Kenya. Wanda hakan zai sa maza masu shaye-shaye rasa ganyen.
A Pakistan wata kotu ta soke hukuncin kisa da aka yankewa wani dan burtaniya akan kisan wani dan jaridan Amurka Daniel Pearl a 2002, da kuma mutane ukku da suma suke fuskantar daurin rai-da-rai.
A Kenya, wasu iyaye a Nairobi sun binne dansu mai shekaru 13 da haihuwa, wanda aka zargi jami’an ‘yan sanda da harbe shi har lahira a barandar gidansu a yayin da suke aiwatar da dokar hana fitar dare.
Fadar White House wacce ta ce yakamata Amurka ta shirya samun mace-mace 100,000 zuwa 240,000 sakamon cutar Coronavirus a cikin watanni biyu masu zuwa koda kuwa Amurkawa sun ci gaba da nesa-nesa da juna.
A Najeriya, sanarwar da Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar ta sanya dokar hana fita na kwanaki goma sha hudu (14) a Legas, birni mafi girma a Afirka, ta sa rububin siyan kayan abinci da yawa, don yin tanadi.
A kasar Indiya, a kalla mutane 24 da suka halarci wani taron addini, a Nizamuddin na New Delhi, an tabbatar sun kamu da cutar coronavirus, in ji wani jami'in lafiya na yankin.
Annobar cutar ta Covid-19 ta na ci gaba da tasiri a Najeriya kamar sauran kasashe, inda hukumomi suka rufe makarantu, sannan suka bukaci mutane da su guji taro a wuraren ibada da sauran sha’anoni. Sai dai wasu mutanen sun ki daukar shawarar ta hukumomi.
Amurka: Shugaba Donald Trump ya kara tsawon dokar hana zirga-zirga zuwa wata daya, a yayin da babban masanin cutuka masu yaduwa na Amurka, Dr. Anthony Fauci, ya yi hasashen cewa Amurkawa 100,000 ko fiye da haka za su iya mutuwa daga cutar annobar coronavirus.
'Yan kasar Mali sun kada kuri'u a jiya Lahadi a zaben majalisar dokoki da aka jinkirta na tsawon lokaci, kusan kwana guda bayan da kasar ta sami mututwar mutuum na farko sanadiyyar coronavirus tare da wani shugaban 'yan adawar da aka sace kuma aka yi imanin yana a hannun mayakan jihadi.
A Birtaniya, an tabbatar da cewa Yarima Charles, mai jiran gadon sarautar Birtaniya, yana dauke da cutar coronavirus, gidan sarautar suka bayyana haka a yau Laraba. Charles, babban dan Sarauniya Elizabeth, yana da shekaru 71 da haihuwa.
Ministan Tsaron kasar Sudan, Lutanal Janaral Jamaleidin Omar Ibrahim ya mutu sakamakon bugun zuciya a Juba, babban birnin kasar Sudan ta Kudu, inda yake halartar tattaunawar zaman lafiya da kungiyoyin ‘yan tawaye, a cewar rundunar soja.
A Japan Shugaban kwamitin wasannin Olympic na duniya Thomas Bach, da Firaiministan Japan Shinzo Abe, suka cimma yarjejeniyar dage wasannin Olympics na Tokyo.
A kasar Maroko cutar Coronavirus na barazana ga ma'aikatan wuccin gadi, wadanda basu da kwangila da kariyar gwamnati a ƙasar
Guinea: Ana ci gaba da kirga kuri'u a zaben da ake ta gardamma akai na bitar kundin tsarin mulkin kasar Guinea da zaben majalissar dokoki bayan da aka kashe wani mutum daya, wasu kuma da dama suka raunata yayin da 'yan sanda suka harba borkonon tsohuwa a lokacin wani rikicin da masu zanga-zanga.
Duniya: Adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a fadin duniya ya kai dubu-dari-biyu-da-casa’in-da-hudu-dari-daya-da-goma (294,110) yayin da adadin wadanda suka mutu ya kai dubu-goma -sha-biyu-da-dari-tara-da-araba’in-da-hudu (12,944) ya zuwa daren jiya Lahadi
A bana an gudanar da bukin kamun kifi na Argugun kuma daya daga cikin manyan al’adun gargajiya na Arewacin Najeriya wanda aka shafe shekaru sama da goma ba’a ayi shiba a sanadiyyar rashin tsaro.
Domin Kari