Amurka: Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya tauttauna da shugabanin yankin kasashen Asiya a California kan harkokin kasuwanci da rikicin yankin tekun kudancin China.
Nigeria: Hukumomin Najeriya sun gana da manyan kamfanonin mai domin samun kudaden fara hakar mai da kuma biya basussuka dala biliyan hudu.
Turkey: Firamininsta Turkiyya, Ahmet Davutoglu ya ce ba zai amince Kurdawan Syria su karbe garin Azaz da ke da nisan tafiyar kilomitoci kadan a iyakar kudancin kasar.
Najeriya: Ministan man fetur din Najeriya, Emmanuel Ibe Kachikwu, ya ce za kara yawan man da ake fitarwa, yayin da shugaban kasa ya himmatu wajen samar da sauye sauye a fannin.
ZABEN 2016 A NIJAR: Kai Tsaye Ga Ouhoumoudou Mahamadou Darektan Yakin Neman Zaben Mahamadou Issoufou Dan Takarar Shugaban Kasar Jam'iyyar PNDS TARAYYA, Da Bayanin manufofin Da Jam'iyar Su Ta Sa A Gaba.
Yar Kasar Australia Jocelyn Elliot da Alqeda ta kama a watan da ya gabata ta koma Burkina Faso tare da shan alwashin ganin an sako mijinta.
Morocco: Sarki Mohammed VI na kasar Morocco ya kaddamar da ma’aikatar lantarki mai anfani da karfin hasken rana ta farko a kasar don bunkasa aiyukkan masana’atun makamashi.
Domin Kari