Kungiyar Al Qaeda ta dauki alhakin kai harin da ya kashe mutane 22, a wajen shakatarwa Grand-Bassam da ke kasar Ivory Coast.
Za'a Sake Janusz Walus Wanda Ya Kashe Shugaban masu adawa da mulkin wariyar launin fata na Afirkata kudu Chris Hani, nan da sati biyu domin ya ci gaba da zaman gyara halinka, bayan ya shafe shekaru fiye da 20 a gidan yari.
Babban Sakarataren Majalisar Dunkin Duniya Ban Ki-moon ya ce dole sai an yanke shawarar daukar babban mataki don kawo karshen fyade da dakarun samar da zaman lafiya na majalisar dunkin duniya ke aikatawa.
An samu wani tsohon sojan sama na Amurka da laifin kokarin bayar da agaji ga kungiyar ISIL, ya zamo tsohon sojan Amurka na farko da aka taba samu da irin wannan laifin.
Nigeria: Ma’aikatan man fetur sunjanye yajin aiki kan shirin rarraba kamfanin man fetur na kasa zuwa gida biyar.
A karon farko tun bayan kauracewa harakokin zabe da 'yan adawar Nijar suka yi Hukumar zabe mai zaman kanta ta Janhuriyyar Nijar ta mayar da martani,a cewar mataimakiyar shugaban hukumar ta biyu Maryama Katambe.
Ana Ci Gaba Da Zanga Zanga A Ofishin Jakadancin Rasha Dake Kiev domin ganin an saki matukiyar jirgin Ukrain Nadezhda Savchenko wacce ta kwashe fiye da shekara a tsare.
Ministan man fetur a Najeriya Emmanuel Ibe Kachikwu ya ce nan da watanni 18 kasar Najeriya Za Ta daina shiga da tacaccen mai cikin kasar.
Kamfanin dillacin labaran kasar Iran ya ce zaratan sojojin Revolutionary Guard, sun yi gwaje gwajen makamai masu linzami a lokacin atisaye da sojoji suka yi.
Akalla Mutane 30 Suka mutu bayan da mayakan sa kai da dakarun Tunisia suka yi wata arangama a garin Ben Guerdane dake kn iyaka da Libya.
Al'umar hamhuriyar Benin na zaben shugaban kasa inda 'yan takara 33 ke neamn maye gurbin shugaba mai barin gado, Thomas Boni Yayi.
A Karo Na Hudu Marie Elise Gbedo ta shiga takarar neman zamowa macen farko da zata shugabanci Jamhuriyar Benin.
Shugaban Turkiya Tayyip Erdogan yana ziyara a Najeriya don bunkaa huldar cinikayya da ta kasuwanci da wannan kasa dake Afirka ta yamma.
Yan sanda sun kashe wasu mata 'yan tsagera su biyu wadanda suka kai farmaki kan wata motar bas ta 'yan sanda, suka kuma jefa gurneti a birnin Istambul.
Shugaban Turkiyya Rajib Tayyib Erdogan ya gana da takwaransa na Ghana a sabon filin saukan jirage na Kotoka da ke Accra yayin wata ziyarar kwanaki biyu.
Sakaratarin harakokin wajen amurka John Kerry yace yan kwanakin dake tafe zasu zamo masu matukar muhimmanci wajen karfafa gurin sassauto da zafin rikicin da ake yi a kasar Syria.
Domin Kari