Jam’iyyar PDM a Kamaru tana bikin cikar shekaru 31 tun da kafuwa, ta hanyar kiran Shugaba Paul Biya da ya tsaya takarar shugaban kasa a 2018.
Hadarin da ya faru a saboda rashin kula na kwarai a wata mahakar kwal dake Arewacin China, ya kashe ma'aikata 19 an kuma ceto mutane 110.
An sake zaben shugaban Jamhuriyar Congo, Denis Sassou Nguesso a wa’adi na uku, wanda hakan ya kara tsawon zamansa na shekaru 32 akan mulki.
Wasu hare-hare da aka kai a filin tashin jiragen birnin Brussels da tashar jirgin karkashin kasa sun halaka akalla mutane 34 kana suka raunata waso fiye da 170.
Wasu 'yan bindiga hudu sun kai hari a hedkwatar horar da dakaru ta tarayya turai dake Bamako a Mali.
Shugaba Barack Obama ya isa birnin Havana a zaman shugaban Amurka na farko dake kan karagar mulki da ya kai ziyara cikin shekaru 88, abinda ya rufe babin kiyayyar da ta wakana tsakanin kasashen biyu tun daga zamanin yakin akida.
Shugaba Mahamadou Issoufou ya jefa kuri'arsa a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa, inda yan adawa ke kira a kaurace ma wa.
Yau ranar 20 ga wannan wata na Maris 'yan kasar Nijar na gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu.A wata hira da yayi da manema labarai Firaministan kasar Birji Rafini yayi fatan cewa, za a samu fahintar juna tsakanin 'yan adawa da masu mulki.’
Yau ranar 20 ga wannan wata na Maris 'yan kasar Nijar na gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu.Shugaban kasar Isufu Mahamadu shi ne ya soma kada kura'arsa a birnin Yamai a runfar zabe mai lamba 001.
Matassa kwararru na kenya suna watsi da aikin ofis suna komawa ga noma wadda a yanzu ta fi riba.
Shugaba Recep Tayyib Erdogan yayi kashedin cewa kasashen Turai fa ba su tsira ba daga harin tsageran kurdawa.
Firai ministan Turkiyya ya yi jimamin wadanda suka rasa rayukansu a harin da aka kai Ankara ranar Lahadi, wanda kungiyar tsagerun TAK sun dauki alhakin kaiwa.
Bom din wanda wasu ‘yan kunar bakin wake mata suka tada sunyi shigar maza ne suka saje da masallata, alokacin da daya daga cikin ‘yar kunar bakin waken ta shiga Masallaci da tada bom din dake jikinta.
Duban mutane sun yi wata zanga zangar nuna kin jinin babban sakataran Majalisar Dinkin Duniya a garin Layounne, saboda yayi amfani da kalmar ''mamaya'' wajen bayyana Yankin Yammacin Sahara da ake rikici kai.
Akalla mutane 15 suka rasa rayukansu a wani harin bam da aka kai a wata motar bas da ke tsaye a Peshawar yayin da hukumomin Pakistan suke zargin kungiyar Taliban.
Yan majalisar dokokin Myanmar sun zabi shugaban kasa farar hula na farko cikin shekaru 50, Mr Htin Kyaw, abunda ya kara kusantar da kasar ga cikakken mulkin demokradiya.
An bude bankin China A Casablanca, da zummar bunkasa zuba sabbin jarurruka a Afirka.
#Niger #Nigeria #Taskar #VOAHausa
Mutane miliyan daya da dubu dari hudu suka fito zanga zanga a Birnin Sao Paulo, domin nuna kyamar zariya da cin hanci da ake zargin gwamnati da aikatawa, tare da neman tsige shugaba Dilma Rousseff mai r'ayin gurguzu.
Domin Kari