Yan sanda sun cafke shugaban ‘yan adawan Uganda Kizze Besigye, yayin da ake zaman dar-dar bayan zaben kasar da aka yi.
Yan majalissar Spain sun yi muhawara akan shawarar firaministan wuccin gadin kasar ta goyon bayan yarjejeniyar tarayyar Turai ta hana 'yan gudun hijira isa Girka.
Bayanin Mataimakiyar Sakataren Harkokin Wajen Amurka mai kula da harkokin Afirka Linda Thomas-Greenfield game da yaki da 'yan ta'addan Boko Haram a Najeriya.
Daya daga cikin shugabanin kasashen Afirka wanda yafi kowa dadewa akan mulki, shugaba Jose Eduardo Dos Santos, yace zai sauka daga mulkin a shekara ta 2018.
Dalibai a Faransa suna zanga zangar kin amincewa da sauye-sauye a fannin kwadagon kasar, inda suka rinka jefa duwatsu da kwayaye, yayin da 'yan sanda ke maida martini da borkonon tsohuwa.
Jirgin kasa na fasinja na Amtrak a nan Amurka ya ci karo da wani taragu da aka bari kan layin dogonsa kusa da birnin Philadelphia, ya kashe mutane 2, wasu 35 suka ji rauni.
Yan bindiga sun kai hari a wata tashar talabijin mai goyon bayan gwamnatin jeki-nayi-ki ta Libya a birnin Tripoli.
TASKAR VOA: Kalli Shirin Taskar VOA Na Wannan Makon Kai Tsaye.
‘Yau 2 ga wannan wata na Afrilu aka gudanar da bikin rantsar da shuagabn Janhuriyyar Nijar Isufu mahamadu bayan ya lashe zaben shuagaban kasar zagaye na biyu da aka gudanar a ranae 20 ga watan jiya na Maris da kashi 92,51% a gaban abokin karawarsa Hama Amadu da ya samu kashi 7,49%.
Akalla 'yan sanda shida ne suka mutu bayan da wani bam da aka boye cikin wata mota ya tashi a kudu a birnin Diyarbakir dake kudu maso gabashin kasar, jami'ai suka ce babu wanda ya dauki alhakin kai wannan hari.
Boko Haram ta kai hari a garin kerewa a arewa maso gabas, a wani matakin ramuwar gayyar farmakin taron dangi na yanki da sojojin kamaru da Najeriya ke kai musu.
Wakilai daga ksashen dunya 50 sun iso Birnin Washington don taron koin tsaron nuclear na hudu da Shugaba Barack Obama yake mai masaukin Baki.
Yan gudun hijira a arewacin Najeriya na fatar komawa gidajensu yayin da sojoji ke kwato yankunan da ,yan ta'adda suka mamaye a baya.
A yayin da ake cikin yanayin barazanar tsaro, Shugaba Francois yayi watsi da shirin garambawul ga kundin tsarin mulkin kasar bayan gaza cimma matsaya tare da yan Adawa.
Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta ce a yanzu barkeawr annobar Ebola A Afirka ta yamma ba wata barazana ba ce ga duniya.
Duban ‘yan kasar Mozambique sun tsere zuwa Malawi, domin su gujewa fada tsakanin ‘yan tawaye da jami’an tsaron gwamnati.
An kama wani mutum da ya karkata akalar jirgin saman kasar Masar bayan da jirgin ya sauka a Cyprus inda aka saki fasinjoji 55 da ke cikin jirgi.
An kashe wani zababben wakili tare da 'yan tawaye 30 a wata angama tsakanin dakarun tsaro da 'yan tawayen PKK a yankin kudu maso gabashin Turkiyya.
An kama mutane biyu da ake zargi da hannu a harin ta'addanci da aka kai a Ivory Coast Inda Mutane Akalla 19 suka mutu.
Sakarataran harokokin waje Amurka John Kerry , ya gana da shugabanin tarayya turai inda ya mika ta'aziyya dangane da harin da aka kai ranar talata a tashoshin jirgin sama da na kasa a Brussels.
Domin Kari