Shugaba Barack Obama ya fara ziyarar Saudi Arabiya da ajanda akan harkoki dabam-dabam ciki har da samun zaman lafiya a yankin.
A kasar Afganistan wasu gungun mayakan kungiyar Taliban sun kai harin bom sun kuma bude wuta, inda suka kashe a kalla mutane 30 da wasu sama da 237.
Mawuyacin halin da mutane suka shiga ya kara ta’azzara, yayin da dumamar yanayin El Nino ya haddasa matsanancin fari.
BRAZIL Kashi biyu bisa uku na'yan majalisar wakilan Brazil sun jefa kuri'ar fara shirin tsige shugaba Dilma Roussef.
An rantsar da dadadden Shugaban Jamhuriyar Kwango Brazaville , Denis Sassou Nguesso, don fara sabon wa'adin shekaru 5 kan mulki.
Kalli shirin Taskar VOA na wannan makon kai Tsaye, A shirin namu na yau, Taskar VOA na dauke da hira ta musamman da kakakin fadar gwamnatin Najeriya, Malam Garba Shehu.
Wata girgizar kasa mai karfin awo shida, ta abku a yamacin kasar Japan, inda ta kashe mutane 9, wasu fiye da 1000 suka ji rauni.
Gwamnati tana neman shigo da man fetur don magance karancin da ya jawo yan kasa suna layin shan mai na dogon lokaci.
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya gana da firimiyan China, Li Keqiang a Beijin, inda ya nemi Chinan ta taimakawa Najeriya wajen farfado da tattalin arzikinta.
Sojojin Faransa da suke aikin kiyaye zaman lafiya su 3, sun mutu bayan da motarsu ta taka nakiya.
An yanke hukuncin dauri a kurkuku ma wasu mutane 12 'yan kungiyar masu ikirarin jihadi mazunin Faransa, bayan da aka cusa masu tsatsauran ra'ayi a wani masallaci a wata unguwa a Paris, mai suna Villiers-sur-Marne.
Mata 'yan Shia sunyi zanga zanga a Kaduna suna neman a sako Shugabansu da wasu da dama da ake tsare da su, tun bayan arangamar da aka yi tsakanin sojojin da mabiya shugaban nasu, lamari da ya halaka kusan mutane 350.
Akalla mutane hudu suka mutu bayan wani harin kunar bakin wake da aka kai a kusa da wani filin wasan kwallo dake Aden na kasar Yemen.
Wani jirgin Norway ya ceto 'yan gudun hijira kusan 300 dake kokarin ketare tekun Bahar Rum, ya kai su tashar jiragen ruwan Taranto a Italiya
Shugaba Hery Rajaonarimampianina ya nada ministan cikin gida Solonandrasana Olivier Mahafaly a matsayin sabon firayim minista.
An kashe wani dalibi shari'a a kasar Bangladesh bayan da ya yi rubutun sukar kishin Islam a shafin Facebook, abinda ya janyo zanga zanga a Dhaka, babban birnin kasar.
Ana gudanar da zaben shugaban kasa yayin da ake sa ran Shugaba Isma'il Omar Guellehzi ci gaba da mulkin da yayi shekaru goma sha bakwai yana yi.
Domin Kari