An kona tan 105 na hauren dabbobi da kudinsu ya kai kusan dala miliyan dari a Kenya, a wani mataki mafi girma a tarihin kona hauran dabbobi a Afrika.
Sai kuma Portugal, inda direbobin Taxi kimanin dubu 6 ke zanga zanga har suka rufe tituna a wasu birane 3, domin nuna rashin jin dadinsu ga zuwan kamfanin Uber.
Tsohon shahararren dan wasan kwallon kafa, George Weah ya bayyana shirinsa na shiga takarar shugaban kasar Liberia ta shekara mai zuwa, wanda shine karo na biyu da ya shiga takarar.
Sojojin Amurka sun kawo ziyara Muryar Amurka, inda suka tattauna da shugabannin sashen Afirka na Muryar Amurka, akan yadda harkokin Afirka ke gudana, musamman game da batun taimako wajen yaki da ta’addanci da kuma samar da abubuwan more rayuwa.
An rantsar da sabon shugaban 'yan Tawayen Sudan ta Kudu Riek Machar a matsayin mataimakin shugaban kasa wanda ake kyautata zato hakan zai wanzarda zaman lafiya bayan kwashe shekaru sama da biyu ana tashin hankali a kasar.
Dakarun Isra’ila sun harbe wata mata da dan‘uwanta har lahira, bayan da aka yi zargin suna dauke da wukaken da za su kai hari a wani shingen bincike da ke yammacin gabar tekun Gaza.
Wani gungun ‘yan bindiga dauke da muggan makamai ya kashe babban janar din Kabilar Tutsi, Athanase Kararuze a lokacin da ya kai ‘yar sa makaranta.
Anyi wani taro a Jami'an Johns Hopkins inda aka tattauna akan dabarun yanda za a shawo kan matsalolin Arewacin Najeriya da suka hada da talauci da rashin aikin yi.
Komandan Rundunar Tsaron Kasashen Yankin Tabkin Tchadi Manjo Janar Lamidi Adeoshun ya kawo wata ziyarar aiki a Jamhuriyar Nijar, wanda ya samu ganawa da Shugaban Hafsan hafsoshin Nijar Janar Seyni Garba.
Shugaban Afirka ta kudu Jacob Zuma ya gana da Shugaba Hassan Rouhani a farkon ziyarar sa Birnin Tehran na kwanaki uku inda ya yabi juyin juya halin Iran na shekarar 1979.
Shugaban Amurka Barack Obama ya gana da shugabannin tarayyar Turai a Jamus don tattaunawa akan batun musayar bayanan sirri da tsaro, biyo bayan hare-haren da aka kai kwanan nan.
Jakadiyar Amurka a majalisar 'Dinkin Duniya, Samantha Power Ta Ziyarci Masu Fafutukar A Nemo Yan Matan Chibok.
Anyi wata ganawa ta musamman tsakanin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da jakadiyar Amurka a Majalisar 'Dinkin Duniya, inda suka tattauna kan muhimman butun yan gudun hijira da yakin Boko Haram.
Kasar Japan Tayi Nasarar Gwajin Wani Jirgin Yakinta a Karon Farko.
Magoya baya sama da dari na madugun 'yan tawaye Riek Machar sun Isa Juba wanda ake fatan zai bada damar dawowarsa.
Gwamnatin Libya ta maida bakin haure sama da 200 zuwa kasashensu, lamarin da ya dakile burinsu na zuwa turai.
Firayim Minista David Cameron ya taya Sarauniya Elizabeth ta biyu murnar cikar shekaru casa'in da haihuwa, yana mai bayyana ta a zaman ginshikin kasar.
Kungiyar agaji ta Red Cross tace jami’an ta uku sunyi batan dabo a Arewacin Mali, inda yawancin kungiyoyin masu tsatstsauran ra’ayi ke zaune.
Domin Kari