Shugaba Mahammadu Buhari yace ba zai nemi David Cameron ya bada hakuri ba kan maganar da ya yayi na cewa Najeriya da Afghanistan na gaba akan cin hanci da rashawa.
Shugaba Recep Tayyip Erdogan yace lallai kasarsa na kan gaba wajen yakar kungiya mai tsatsauran ra’ayi na IS bayan da ya shaida cewa dakarun Turkiya sun kashe mayakan IS dubu uku a Syria da Iraqi.
Wani jirgin yakin ruwan Amurka ya yi tafiya a kusa da tekun kudancin China da ake takadamma akai, lamarin da ya janyo fushin ma’aikatar harkokin wajen China.
Ana binciken shugaban ‘yan adawan Jamhuriyar Dimokradiyar Congo, Moise Katumbi, bisa zargin cin amanar kasa da arangamar da magoya bayansa suka yi da ‘yan sanda.
A yau Talata, shugaban Amurka Barack Obama, ya ce zai kai ziyara Hiroshima a karshen wannan wata, inda zai zama shugaban Amurka na farko da zai je birnin na Japan, wanda wani jirgin yakin Amurka ya jefa makamin kare dangi na farko a shekara ta 1945.
Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya zargi manyan kasashen Duniya dake yakar kungiyar ISIL a Arewacin Siriya, cewar sun kasa taimakawa gwamnatinsa tayi yaki a kasarta.
Uwargidan tsohon shugaban kasa Simone Gbagbo za ta fuskanci shari’a akan laifin hannu a cikin tashin hankali da ya biyo bayan zaben shekarar 2010 da mutane 3000 suka rasa rayukansu.
A cikin shirin mu na wannan makon mun ziyarci jahar Plateau inda 'yan kabila Irigwe suke bikin maraba da damuna.
WASHINGTON, DC—Shugaban jam’iyyar Republican na Amurka yace yana ganin cewa yanzu ta tabatta da cewa kusan Donald Trump ne wanda jam’iyyar zata tsaida a matsayin dan takarar shugaban kasa bayan da ya sami nasara a zaben fidda gwanin da aka yi jiya a jihar Indiana.
Jam’iyar Ma’aikata mai mulki a Koriya ta Arewa ta gudanar da taronta na farko cikin shekaru 36, karkashin shugabancin Kim Jong Un, sai dai an hana ‘yan jarida kusantar taron.
South Sudan: Jakadiyar Majalisar Dinkin Duniya Zainab Hawa Bangura ta bukaci gwamnati ta hukunta sojojin da ake zargi da aikata fyade.
Masu ayyukan ceto a Nairobi, kasar Kenya sun sake gano wata mata
Amurka da Rasha sun jagoranci cimma yarjejeniyar tsagaita wuta na sa’oi 48 tsakanin gwamnatin Syria da yan tawaye a Birnin Aleppo, inda mummunan fada ya kai ga hallaka farar hula 280.
Masu Ayyukan ceto a Nairobi, kasar Kenya sun sake gano wata mace da rai daga cikin baraguzan ginin da ya fadi kusan mako guda da ya gabata, wanda ya hallaka mutane akalla 26.
Shugaban kasar Mauritania, Mohamed Ould Abdel Aziz ya bayyanawa kasar cewa za ayi zaben raba gardama domin rushe majalisar dokoki a kasar.
Dubban mutane sun guru data gidajensu bayan da wutar ta ci garin Fort McMurray wanda ya tilasta mazaunan garin da su nemi tsira a arewacin yankin.
Yan jarida da masu gwagwarmayar neman yancin kafofin yada labarai na bukin ranar yan jarida ta Duniya
Mayakan I.S sun kashe wani sojan Amurka a Arewacin Iraqi bayan da suka kusta kai cikin dakarun kurdawan Iraqi.
Masu ayyukan ceto sun zakulo wata yarina 'yar shekara daya daga baragizan ginin da ya rushe a Nairobi a ranar Juma'a.
Dubban Mafusatan Masu Zanga-Zanga Sun Mamaye Unguwar Ma'aikatan Diflomasiyya da ke Baghadaza da ake kira Green Zone, bayan da 'yan majalissar kasar suka ki amincewa da sabbin ministoci.
Domin Kari