Wasu tsagerun Niger Delta sun dauki alhakin fasa bututun man fetur mallakar Gwamnati, amma 'yan sanda sun musunta hakan da cewa tsiyayar mai ne ta sanya bututun yin bindinga.
Wata kotu a India ta yankewa mutane 11 hukuncin daurin rai-da-rai, bayan da aka same su da laifin kisan musulmai da dama a boren da aka yi a Gujrat a shekarar 2002, rikicin da wasu suka yi kirarin ya salwantar da rayuka 2,500.
Rundunar Sojin Misra ta ce an gano tarkacen jirgin saman EgyptAir a tekun bahar rum.
Rundunar Sojojin Najeriya sun kara ceto wata yarinya daga Boko Haram, shugaba Mohammadu Buhari ya gana da Amina Ali, Dalibar makarantar Chibok da aka ceto.
Dakarun Najeiya sun fitr da wani hoton bidiyoda ya nuna yadda Amina Ali Darsha Nkeki ta dadawo gida, shekaru biyu bayan da kungiyar Boko Haram ta sace dalibai 219 a Chibo.
Da alamun wani jirgin saman fasinja dauke da mutane 66 wanda ya taso daga Faris zuwa Al-Qahirah, ya fada cikin tekun Bahar Rum, yayin da ake ci gaba da nemansa.
Dubban mutane a Kenya sun fantsama neman gidajen da zasu zauna, bayan da jami’ai a kasar suka fara rushe gine gine da ake ganin nada hatsari har 258 a Nairobi, biyo bayan faduwar ginin daya hallaka mutane 51 a makon da ya gabata.
'Yan sanda sun yi zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da tsanar 'yansanda da ake yi; yayin da kuma wasu muatne kimanin 300 su ka kaddamar da zanga-zanga kishiyar ta 'yansandan, bayan sun yi biris da hana su da aka yi, su ka banka ma motar 'yan sanda wuta.
Likitocin agajin jinkai na Operation of Hope na kasar Amurka suna aikin tiyatar gyaran lebe a Bulawayo a kasar Zimbabwe
A kasar Najeriya gwamanti na nemar cimma jituwa da shugabannin kungiyoyi don kauce ma zanga-zanga a fadin kasar saboda karin farashin man fetur.
Amurka da kawayenta suna kokarin ganin an cire takunkunmin makamai ma kasar Libya, don ta iya taka burki ma ISIS da sauran kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi.
Jirgin sama mafi girma a duniya na Antonov ya sauka kasar Australia a karon farko, yayinda dubban mutane suka taru don kallo.
Tsohon wanda ya jagoranci juyin mulki a kasar, Azali Assoumani shi aka zaba a matsayin Shugaban Kasar Comoros bisa sakamakon wuccin-gadi.
A China girgizar kasa mai karfin 5.5 ta afkawa kauyen Kata, inda ma’aikatan ceto ke aikin kwashe mutane 4,200 zuwa wani sansanin wucin gadi.
Farashin man fetur ya karu da kashi 67 cikin dari, yayin da faduwar farashinsa a duniya ya shafi tattalin arzikin kasar, al'amarin da ya haddasa karancin dala.
Yau ne Sabuwar Direktar Muryar Amurka, Amanda Bennett, ta kai wa Sashen Hausa ziyara inda ta tattauna da mai'aikatan Sashen Hausa a kan ayyukansu na bada labarai zuwa ga masu sauraren Sashen Hausa a duk fadin duniya.
Kungiyar unkasa tattalin kasashen yammacin Afirka ta fara taron kwanaki uku a Nijar, domin tattaunawa kan matsalolin da suka shafi fannin yawon bude ido.
Shugaba Dilma Rousseff ta fuskanci shari’a bayan da majalisar dattawa suka kada kuri’a inda aka samu rinjaye akan tsige ta daga mukaminta kuma mataimakinta Michel Temer zai zama shugaba mai rikon kwarya.
Shugaba Mahammadu Buhari yace ba zai nemi David Cameron ya bada hakuri ba kan maganar da ya yayi na cewa Najeriya da Afghanistan na gaba akan cin hanci da rashawa.
Domin Kari