Dakarun saman Najeriya na amfani da wata fasahar zamani, wajen fatattakar mayakan Boko Haram daga arewa maso gabashin kasar.
Firai ministan Turkiya ya ce akwai alamu Kungiyar IS ce ta kai harin da ya halaka mutane 41 a filin jirgin saman Ataturk na Istanbul.
Uwargida Michelle Obama ta kaddamar da wani rangadin kasashe uku domin jan hankulan ‘yan mata su cigaba da neman ilimi.
Dakarun gwamnati da ‘yan tawayen Houthi sun yi arrangama a dutsen Nehm a cigaba da rikicin kasar da ya kashe mutane 41 a sassa dabam-dabam a karshen makon da ya wuce.
A bidiyonsa na farko cikin watanni 22, shugaban kungiyar Ansar dine, Iyad Ag Ghaly, ya yi barazana ga Faransa da dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Mali.
Hare-haren kunar bakin wake da wasu mahara su 3 suka kai a al-Qaa, wani gari da kristoci suka fi yawa kusa da iyakar Lebanon da Siriyya, ya kashe akalla mutane 5 wasu su 19 kuma sun jikkata.
Hirar kwamishinar mata ta jihar Filato Rofina Gurunyen a wata ziyara da ta kawo sashen Hausa na Muryar Amurka
Babban Taron Wayarwa Da Matasa Kai Wajen Yakar Mugayen Dabi’u Da Illar Zaman Banza A Jihar Yobe
Ra'yoyin wasu mutane daga jihar Kano, kan yadda lamarin rayuwa cikin watan Ramadan mai albarka
Jama'a a Malawi Sunyi Zanga-Zanga Saboda Hare Haren da Ake Kaiwa Zibiya.
Burkina Faso ta kaddamar da gina wata babbar tashar samar da lantarki daga hasken rana da zata lashed alar Amurka Miliyan 50, sannan mafi girma a yankin Sahel dake hamada.
Wani kamfani a Jamhuriyar Nijar na markada gyada don taimakawa mutanen da Boko Haram ta raba da muhallansu, da kayan da zai kara musu lafiya.
‘Yan sandan Faransa sun haramta yin zanga-zanga a Paris, sa’oi 24 gabanin tattakin da kungiyar kwadago ta shirya yi, lamarin da ya haifar da fargabar aukuwar rikici.
Jami’an gwamnatin Jamhuriyar Tsakiyar Afrika da dakarun rundunar hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya ta MINUSCA, sun bayyana tsauraran matakan tsaro a rikicin Bangui da ya halaka mutane uku.
Darajar Naira ta fadi bayan da gwamnati ta cire hannunta a hadahadar kudaden kasashen waje.
US: Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry tare da shahararriya ‘yar fim Angelina Jolie sun tattauna matsalar karuwar 'yan gudun hijira a duniya yayin da yanzu yawansu ya kai kashi 1 cikin 100 na al'ummar duniya.
Nigeria: Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo daga Landan inda ya je neman maganin ciwon kunne.
Ana cigaba neman mutane masu rai bayan ambaliyar da ta auku a Java inda mutane akalla 43 suka mutu da yawa kuma suka rasa matsugunnansu.
Domin Kari