Babban Sakataren Majalisuar Dinkin Duniya, Ban Ki- moon ya yi kira ga kwamitin sulhun majalisar duniya, da ya saka takunkumin sayen makamai cikin gaggawa akan Sudan ta Kudu.
An kashe mutane akalla 276 a kazamin rikicin da ya barke a Juba, babban birnin Sudan ta Kudu, tsakanin dakarun Shugaba Salva Kiir da na mataimakinsa Riek Machar.
Firai ministan India Narendra Modi ya kai ziyara Tanzania a zango na uku na rangadin kwanaki biyar da ya ke yi a kasashen Afrika, wanda ke kara nuna zawarcin da kasarsa ke yi da nahiyar.
Yan sandan birinin Dallas dake jihar Texas sun ce an kama mutane uku, na hudunsu kuma ya mutu, bayan da 'yan kwanbton-bauna suka kashe 'yan sanda biyar a wani hari lokacin da ake yin zanga-zangar lumana.
Gwamnati Sudan ta Kudu, ta soke bikin ranar samun ‘yancin kai, yayin da kasar ke fama da yakin basasa da yunwa da matsalar tattalin arziki.
Anyi hawan Durbar a Birnin Kano, kamar yadda aka saba duk shekara a karamar sallah yayinda musulmi a duk fadin duniya suka kammala Azumin watan Ramadana.
‘Yan sanda a Louisiana sun yiwa wani bakar fata Alton Sterling mummunan harbin da ya janyo zanga zangar zargin ‘yan sandan da muzgunawa bakaken fata ta hanyar harbinsu.
Musulmi a Afrika da sauran sassan duniya sun yi bikin sallar eid ul fitr, bayan kammala azumin watan Ramadana.
Hukumomin na Saudiya har ila yau na ci gaba da binciken wani harin kunar bakin wake da aka kai a wani masallacin ‘yan Shi’a a gabashin birnin Qatif, inda ministan cikin gidan ya ce an gano wasu sassan jikin mutane uku, amma ba a gane ko su wanenene ba.
Hamshakin mai kudi da ya fi kowa arziki a Afrik, Aliko Dangote, na shirin zuba jarin dala biliyan 12 domin bude matatar mai nan da shekarar 2019.
Jakadan kasar China a Congo, yace Shugaba Denis Sassou N'Guesso da takawarsa na kasar China Xi Jinping, na shirin tattaunawa akan matsalolin zaman lafiya a nahiyar Afirka ta tsakiya a yau Talata.
Jami’ai a Isra’ila sun harbe wata mata har lahira, bayan da akace tayi kokarin cakawa wani jami’in dan sanda wuka, kwana daya kenan bayan da aka kashe wata yar shekaru 13 da wuka.
Nigeria: Mafi wadata a nahiyar Afirka, Aliko Dangote yana shirin zuba jarin dala biliyan 12 kafin shekarar 2019 don kaddamar da matatar danye mai ta farko a Najeriya.
Shugaba Benigno Aquino ya sauka daga kujerarsa a wani bikin barin gado, inda ya mika mulki ga magajinsa Rodrigo Duterte.
Shugaban ‘yan adawa a Uganda Kizza Besigye ya bayyana a koto, inda ake tuhumarsa da laifin cin amanar kasa, bayan da ya hada taron ranstsar da shugaban kasa na bogi.
Taron tattauna muhimmancin kuri’un yan Afirka mazauna Amurka a zaben shugaban kasa a da za’ayi.
Domin Kari