Hirar Sahabo Imam Aliyu da Melanie Dickson, wata 'yar birnin Cleveland da ta halarci babban Taron Jam'iyyar Republican.
An dawo da ‘yan kamaru goma sha uku da wasu yan tawaye suka sace su bara zuwa birnin Younde inda ake duba lafiyarsu.
An Yanke Hukumcin daurin Shekaru 14 Kan Matar Da Ta Kashe 'Ya'yanta 4 a Kasar Jamus
Wani dan gudun hijira mai shekaru 17 daga Afghanistan ya sassari fasinjojin wani jirgin kasa da gatari a kudancin Jamus, ya raunata mutane hudu. Kungiyar ISIS ta dauki alhakin harin.
Sabon sufeto janar na 'yan sandan Najeriya, Idris K. Ibrahim, ya kai ziyara a Jihar Borno, inda ya ziyarci gwamna da Shehun Borno da kuma wani sansanin 'yan gudun hijira dake babban birnin.
An cimma wata yarjejeniya a birnin Yamai na Janhuriyar Nijar tsakanin kungiyar 'yan tawayen kasar Mali CMA da kuma wasu kungiyoyi dake goyon bayan gwamnati Mali, Kaoucen Maiga daya daga cikin tsofofin 'yan tawayen Nijar, ya bayyanawa Muryar Amurka irin tasirin da yarjejeniyar zata yi.
An samu tsagaitawar wuta a Sirte bayan da aka kashe wasu mayakan da ke marawa gwamnatin hadakar Libya baya su 20, kana aka jikkata wasu 100 a arangamar da suka yi da mayakan ISIS.
Ofishin kula da shige da ficen baki yana fama da dimbim baki masu kokarin neman aikin yi ko kuma yunkurin ketarawa zuwa Turai.
Wani harin bindiga a Louisiana ya halaka ‘yan sanda uku ya kuma raunata wasu uku, lamarin da ya kara nuna ci gaban hare-haren da ake kaiwa ‘yan sanda, bayan harbe-harbe masu cike da takaddama da su ke yi.
Direban wata babbar mota ya kashe mutane 84 a garin Nice da ke Faransa, bayan da ya bi ta kan tarin jama’r da ke bikin Bastille na zagayowar ranar da kasar ta fuksancin juyin juya hali, harin da aka alakanta da ta’addanci.
Shugaba Salva Kiir ya yi kira ga ‘yan adawa da su zo a tattauna domin kada yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma ta samu cikas daga rikicin da ya barke kwanannan.
Wani da ake zargi mai daukan mayaka ne na kungiyar al-shabab ya kashe 'yan sanda hudu a wani caji ofis a Kenya, bayan da ya kwace bindigar wani mai gadi.
Adadin wadanda suka mutu a rikicin Juba, babban birnin Sudan ta Kudu ya kai akalla mutane 272, ana kuma tunanin zai karu yayin da likitoci ke kokarin ceto rayukan wadanda suka ji rauni.
Firai ministan Birtaniya, David Cameroon, ya mika godiyarsa ga ‘yan majalisar dokokin kasar, yayin da ya ke jawabin ban kwana na barin mukaminsa, bayan da Birtaniyar ta jefa kuria’r amincewa ta fice daga tarayyar turai.
Jirgin sama mai amfani da hasken rana, ya sauka a Birnin Al Qahirah inda yake gab da kammala rangadin da ya ke yi a duniya.
Akalla mutane 12 sun mutu da yawa kuma sun jikkata bayan da wasu jiragen kasa guda biyu na fasinja suka yi karo da junansu a kudanci kasar Italiya. Har yanzu ba a tabbatar da sanadiyar hatsarin ba.
Domin Kari