Hira da Senator Ken Nnamani da ga jihar Enugu, Najeriya, kan muhimmancin tarukan Jam’iyyun Siyasa na Amurka.
Hira da shugaban gamayyar bakaken fata A majalisar dokoki da ga North Carolina Najeriya G. K Butterfield, kan muhimmancin tarukan jam’iyyun siyasa na Amurka.
US: Tsohuwar Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton ta zama mace ta farko da wata babbar jam’yya a Amurka ta tsaida da ita ‘yar takara a tarihin kasar.
Hira da Raila Odinga, Tsohon Firai Ministan Kenya, Kan Muhimmancin Tarukan Jam’iyyun Siyasa na Amurka da ya yi da wakiliyarmu Grace Alheri Abdu a Philadelphia.
Jami’an tsaro sun ce wani limamin kirista tare da mahara biyu sun mutu bayan da maharan dake rike da wukake, suka yi garkuwa da mutane da yawa da cikin wata majami'a a Normandy.
An yi fito na fito tsakanin ‘yan sanda da magoyan bayan Bernie Sanders a kofar zauren babban taron jama’iyyar Democrat a Philadelphia.
Mutane 13 ne suka halaka bayan wani harin kunar bakin wake da kungiyar Al Shabab ta kai a kusa da gine-ginen Majalisar Dinkin Duniya da na tarayyar Afrika da ke Mogadishu.
Dan Majalisar Wakilan Tarayya, Raul Grijalva, Na Jihar Arizona Kan Taron Democrats
Dubban mutanen da suka rasa matsugunnansu sanadiyyar fadan a Sudan ta Kudu na fuskantar matsalar samun matsugunni a sansanonin Majalisar Dinkin Duniya lokacin damina.
Ana Shirin Fara Babban Taron Jam'iyyar Demokrat Yau A Philadelphia A Nan Amurka
A wannan makon, Shugaba Buhari zai ƙaddamar da sabon layin dogon da ya haɗa babban birnin Abuja da garin Kaduna.
Hira da Aliyu Mustapha Sokoto, Manajan-Edita na VOA Hausa, kan muhimmancin tarukkan jam’iyyun siyasa na Amurka don tsayar da ‘yan takarar zaben shugaban kasa.
Dubban masu zanga zanga sun yi maci a titutuna birnin Istanbul, don nuna goyon bayansu ga shugaba Tayyib Erdogan da kuma yin Allah wadai da yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba.
Kungiyar agajin likitoci ta MSF tayi gargadincewa 'yan gudun hijira dubu 70 suna fuskantar matsananciyar yunwa a garin Dikwa dake arewa maso gabashin Najeriya.
Rana Ta Uku: Babban Taron Jam'iyyar Republican a Garin Cleveland da ke Jihar Ohio.
Daruruwan mutane a Tripoli sun yi zanga zangar nuna adawa da kasancewar dakarun Faransa a kasar, bayan da wasu sojojinta uku suka mutu a wani hadarin jirgi mai saukar ungulu a Benghazi.
Daruruwan mutane a Juba suna zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da shirin Kungiyar Tarayyar Afirka na tura sojojin kiyaye zaman lafiya na yanki zuwa babban birnin.
Domin Kari