Wani dan shekaru 19 ya soka ma wasu mutane 6 wuka, inda ya halaka daya daga cikinsu kana ya raunata 5 a tsakiyar London, amma jami’a sun ce harin ba na ta’addanci ba ne.
Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ya bar sakon muryarsa inda ya ce har yanzu shi ke jagorancin kungiyar duk da cewa rohotanni sun bayyana cewa kungiyar Daesh (ISIS) ta nada wani wanda zai maye gurbinsa.
Dakarun gwamnatin Siriyya da taimakon jiragen saman yakin Rasha sun kaiwa "yan tawaye hari a kusa da birnin Aleppo biyo bayan zargin cewa an bide wani gari kusa da birnin da iska mai guba.
Sojoji suna cigaba da arrangama da Kungiyar Daesh (ISIS) wajen kwato garin Sirte.
Mahaifin musulmin sojan Amurka nan da yam utu a shekarar 2004 a Iraqi, Khizr Khan, ya gayawa Muryar Amurka cewa takaddamarsa da Donald Trump na haifar da sakamako mai kyau.
Dan wasan Tennis din Nigeria Segun Toriola na shirin zuwa gasar Olympics a karo na bakwai, wanda shi ne dan Afrika na farko da ya samu shiga gasar da zimmar lashe kyauta.
YALI 2016
Somalia: Kungiyar Al-shabab ta dauki alhakin hare-haren da aka kai a wani ofishin ‘yan sanda da suka halaka mutane 10 a Mogadishu.
Magoyan bayan yan jam'iyyar adawa sun yi zanga zanga a wajen ginin majalissar kasar da ke kinshasa, suna nuna rashin amincewarsu da shugaba Joshep Kabila wanda wa'adinsa ya kare tun cikin watan disamba.
Yan Jarida 21 cikin 89 da aka kama bayan yunkirin juyin mulkin da bayi nasra ba sun bayana a kotu.
Dakarun Libya sun yiwa mayakan ISIS kawanya a wani dan karamin yanki a birnin Sirte da ke gabar teku, sun kuma ce suna gab da kwato ikon birnin baki dayansa.
Hira da Kashimana Ahuwa daya daga cikin Magoyan Bayan Bernie Sanders, Kan Muhimmancin Tarukan Jam’iyyun Siyasa na Amurka.
Rasha ta amince ta yi aiki da gwamnatin Syria domin kaddamar da wani babban aikin jin kai da zai tallafawa fararen hula a Aleppo.
Hira da Winnie Odinga daga Kenya, kan muhimmancin tarukan jam’iyyun siyasa na Amurka.
Hira da Barr Sharon Ikezu daga Najeriya, kan muhimmancin tarukan jam’iyyun siyasa na Amurka.
Hira da senata Binta Masi Garba daga Najeriya, kan muhimmancin tarukan jam’iyyun siyasa na Amurka.
Kungiyar likitoci ta dunuya, ta ce ya kamata Najeriya ta zamanto ta farko a cikin wadanda Majalisar Dinkin Duniya za ta baiwa taimakon gaggawa da sabowa wadanda mayakan Boko Haram suka jefa cikin kangi.
Domin Kari