Cikin shirin wannan makon za mu kawu muke ziyarar uwargidan shugaban kasar Najeriya Hajiya Aisha Buhari da ta yi a Amurka da kuma Budewar wani katafaren asibiti mafi girma a yammacin Afrika a Niamey babban birnin kasar Niger.
Bolivia: Ma’aikatan hakar ma’adinai a Bolivia sun yi arangama da ‘yan sanda yayin da su ke zanga zangar zargin gwamnati da hanu a harkokin nuna fifiko ga ‘yan uwansu da abokanai a kamfanonin da su ke aiki a La Paz.
Jirgin kasan da ya hade Abuja da Kaduna ya fara aiki, wanda ya fara nuna sabbin sauye-sauyen ababen more rayuwa da tattalin arzikin kasar.
Hirar Alhaji Idris Mohammed Madakin Jan kuma tsohon Shugaban PHCN a Kadunan Najeriya da wakiliyar VOA Hausa Medina Dauda a Ofishin mu da ke Abuja
Mutane bakwai ciki har masu kashe gobara hudu, sun ji rauni a wutar dajin da ke ci a kudancin Faransa wacce ta fara ci ranar 10 ga wannan wata na Agusta, inda aka kwashe daruruwan mutane.
Rohoton hukumar kula da ‘yan gudun hijra ta Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa daruruwan mutane sun rasa rayukansu, dubbai kuma sun gudu daga gidajensu sakamakon tashe-tashen hankula tsakanin makiyaya Musulmai da manoma Kirista.
Daruruwan mutane sun taru a Moscow don yin zanga zanga kan wata sabuwar doka da suka ce ta take hakkin bayyana ra’ayi a kafar internet.
Nigeria: Nada Abu Musab al Barnawi da aka yi a matsayin sabon shugaban kungiyar Boko Haram, ya haifar da rarrabuwar kawuna a kungiyar, tare da nuna irin matsin da dakarun Chadi da Nijar da Kamaru da Najeriya ke yi akansu.
A tafiyarsa ta farko tun yunkurin juyin mulkin da aka so yi, Shugaba Erdogan ya hadu da Shugaba Putin a Moscow domin gyara dangantakar kasashen biyu wadda ta yi tsami a 2015
Sabon kamfanin nan mai sarrafa shara na Wecycler na fatan hada kai da mazauna Legas wajen basu makin da zai kai su ga samun kyaututtuka.
Akalla mutane 60 ne suka muta wasu 160 suka ji rauni, bayan wani bom da ya tashi a kudu masu yamancin birnin Quetta.
Shugaban boko haram Abubakar Shekau ya sha alwashin ci gaba da fada a wani sabon bidiyo inda yayi watsi da batun rarrabuwar kan kungiyar.
Kwamitin Wasannin Olympics ta Duniya ta kyale "yan wasan kasar Rasha su 271 su shiga wasannin Olympics na Rio, amma ta haramtawa wasu 'yan wasan su 118 a bayan abin fallasar shan maganin kara kuzari da ake tuhumar gwamnatin kasar da basu.
Nigeria: Wani sabon Kampani a Lagos yana taimakawa wajen ceton rayukan mutane ta hanyar manhajarsa Lifebank, inda yake tallafawa wajen neman jini da kuma tafiyar da shi cikin kasar.
Domin Kari