Dakarun saman Najeriya sun ce sun kashe mayakan Boko Haram kusan 300 ciki har da shugabansu Abubakar Shekau a ranar 19 ga watan Agusta.
Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, ya gana da shugabannin addini a Sokoto, inda ya ce yaki da Boko Haram na bukatar yadda da aminci tsakani mutane da gwamnati.
Dakarun Libya sun kwato wasu gine-gine a birnin Sirte da ke karkashin ikon 'yan IS tun bara.
Hukumar da ke kula da inganci kayan abinci ta kai samame shagunan 'yan kasuwan Damagaram inda ta kwace tare de kona kayyakin da suka lalace.
Kungiyar Linx Nigeria ta horar da matasa matakan yaki Da taaddanci a jihar Plateau dake Nigeria
An yi bikin ranar ma’aikatan jin-kai a yankin Diffa na Nijar a yau Alhamis, inda kungiyoyin ba da agaji suke kokarin samar da dubban kudade domin wadanda rikici ya daidaita.
LIBYA: Wasu ma’aikatan jin kan Spaniya, sun kubutar da bakin haure da dama daga wasu kwalekwale uku da suka kusa nutsewa a gabar tekun Libya.
‘Yan sandan Mali sun kashe wani mutun har lahira bayan da suka bude wuta akan wasu masu zanga zanga a lokacin wani boren nuna adawa da kama wani dan jarida Mohammed Youssouf Bathily mai caccakar gwamnati.
Sabon mataimakin shugaban kasar Sudan ta Kudu, Taban Deng Gai na shirin hade dakarun gwamnati da na 'yan tawaye, da zummar kawo karshen tashin hankalin da ake yi a kasar.
Ma'aikatar tsaron kasar Rasha ta ce jiragen yakinta sun yi amfani da filin jiragen yakin kasar iran wajen kai farmaki a Syria, abinda Amurka ta nuna damuwa akai.
Wani dan Saudiyya da Bafalasdine, sun kirkiro wani faifain samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana, wanda zai rika baiwa mahajjata damar yin cajin wayoyinsu.
An dauke 'yan gidan yari guda 15 zuwa hadaddiyar daular larabawa daga gidan kason Amurka dake Guantanamo bay, kasar Cuba. Wannan shine adadi mafi yawa da aka kwashe a lokacin shugaba Barack Obama.
An nunawa mahajjatan Najeriya fifiko wajen ba da canjin dala, duk da faduwar darajar da naira ke fuskanta.
Maus zanga sun yi arangama da 'yan sanda kwanaki biyu ke nan a titunan birnin Milwaukee, jihar Wisconsin bayan da wni dan sanda ya harbe Sylville dan shekaru 23 sau biyu har lahira ranar asabar.
Wani hoton bidiyo da aka wallafa ranar 14 ga watan Agusta , ya nuna wasu daga cikin 'yan matan Chibok na raye, inda Boko Haram ta kuma nemi a yi musayar fursononi.
Domin Kari