Tanzania/Uganda: A kalla mutane 16 suka mutu, 253 kuma suka jikkata bayan da girgizar kasa mai karfin maki 5.7 ta abku a arewa maso yammacin Tanzania, ta kuma ruguza gidaje a tsallaken iyaka a cikin Uganda.
Bakin haure 500 daga cikin 3,400 sun isa Sicily, bayan wasu ayyukan ceto kusan 30 da masu gadin gabar tekun Italiya suka yi a karshen makon da ya gabata a teku meditareniya.
A cikin shirin namu na yau za ku ga yadda wani ma'aikacin tsaron Amurka dan asalin Afrika da ke limanci a ma'aikatar tsaro ta Pentagon.
Shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita, ya hadu da shugaban ‘yan adawa, Soumaila Cisse domin tattaunawa kan batutuwan tsaro da kuma ranakun da za a yi zaben da ke tafe.
North Korea: Gidan talbjin din Korea ta arewa ya ce kasar ta gudanar da gwajin makamin nukiliya mafi girma a karo na biyar.
Ana gina wata cibiyar kula da yara kanana, domin 'yayan mayakan kungiyar Boko Haram, saboda su samu tarbiya ta gari.
Miliyoyin musulmi sun taru a Makka domin gudanar da aikin Hajji, wanda ake sa ran tattalin arzikin kasar zai bunkasa da biliyoyin daloli.
Wata tsohuwar gadar karfe mai kimanin shekaru dari dake layin dogon Abidjan zuwa Ouagadougou ta rushe da jirgin kasa mai daukar kaya akan ta amma babu wanda ya rasa rai.
A Maiduguri da ke jihar Borno ana aikin mayar da 'yan gudun hijira da suka fito daga Konduga shekaru uku bayan da suka tsere daga gidajensu domina kaucewa rikicin Boko Haram.
Rundunar Sojin Najeriya na fafatukar samar da tsaro a garuruwan da su ka kwato daga mayakan Boko Haram.
Shugaba Barack Obama ya kai ziyara a Laos, bayan da ya bayyana cewa Amurka za ta ba da tallafin milyan 90 domin share nakiyoyin da aka dasa da basu tashi ba a lokacin yakin Vietnam.
Shugaban Rasha Vladimir Putin ya bukaci magadan Shugaban Uzbekistan Marigayi Islam Karimov da su ci gaba irin tsarin mulkinsa da kuma hadin kan da ya ke yi Rasha.
Zaben shugaban kasar Gabon ya haifar da fushi akan Hausawa da Musulman Bitnam masu karamin rinjaye, bayan da masu zanga zanga suka zarge su da marawa shugaba Bongo baya.
Hotunan Yaye Bikin 'Yan Sandan Nijer Da Dakarun Amurka Suka Horar
A Cikin shirin na wannan makon za ku ga yadda sansanonin 'yan gudun hijra a Maiduguri ke fuskantar yunwa
Gwamnatin Sudan ta Kudu ta yarda da karin dakarun wander da kaman lafiya dubs 4 a kasar a want kokarin gujewa takunkumi daga Majalisar Dinkin Duniya
Duban mutant sun taro a baking login Issyk-Kul don su kale wasani gargajiya da makiya ke yi.
Mother Teresa yar garin Calcutta, da ta shahara wajen ta sadaukar da kanta wajen taimakawa talakawa ce ake shirin ayyanawa a matsayin waliyar Cocin Roman Katolika a shagalin da za yi a fadar Paparoma ta Vatican ran 4 ga watan satumba.
Domin Kari