Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar PDP, kamar dai yadda da dama daga cikin masu lura da al'amuran yau da kullum da kuma siyasar Najeriya su ka hango.
Tuni dai masu tsokaci a siyasar Najeriya, da kuma sauran 'yan kasa, su ka shiga tofa albarkacin bakunansu kan abin da ake ganin zai faru da kuma wanda ya fi cancanta ko kuma zai ci zaben tsakanin Shugaba Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya da kuma Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Atiku Abubakar na babbar jam'iyyar adawa, PDP.
Ga dai wakilinmu a Kanu Mahmud Ibrahim Kwari da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5
Zaben 2019 Na Najeriya: Za a Buga Tsakanin Buhari da Atiku
Your browser doesn’t support HTML5
Zaben 2019: Za a Buga Tsakanin Buhari da Atiku