Shugaba Kabila ya yi wannan jawabi ne ga al’umma ta telbijin kasar a jiya Alhamis inda ya tabbatar da cikakken mutunta kudin tsarin mulkin kasar.
Sai dai yan adawa sun bayyana shakkunsu cewa zai nemi ya ci gaba da derewa bisa mulki.
Patrick Muyay dan majalisa na jami’aiyar adawa ta PALU yace fahimtarsa, dokokin kasa sun biwa shugaban kasa damar mulki tsawon wa’adi biyu, a don haka yake ganin Kabila zai iya shiga takara.
Wa’adi mulkin Kabila na biyu a matsayin zababben shugaba na karewa ne a 2016. Amma tashe tashen hankula da ayyukan yan bindiga da matsalolin shirya zabe, sun sa an dakatar da gudanar da zabe har sau biyu.
Kabila ya jagorancin DR Congo tun lokacin da aka kashe mahaifinsa Laurent Kabila a shekarar 2001.