NIAMEY, NIGER - Wannan na zaman ci gaba da yunkurin warware rikicin siyasar da kasar ke fama da shi bayan kifar da gwamnatin zababben Shugaba Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yuli.
Wasu daga cikin Malaman Addinin Islama da suka kai ziyarar sulhu Nijar
A wata hira ta musamman da Muryar Amurka Jagoran tawagar Sheik Abdullahi Bala Lau, ya ce akwai alamun haske a kokarin sasanta bangarorin.
Daya daga cikin Malaman Addinin Islama da suka kai ziyarar sulhu Nijar
"Wannan ci gaba ne na kai da komowa a tsakanin Najeriya da Nijar, a matakin riga kafin hana shaidan samun rinjaye a rikicin siyasar da ya biyo bayan juyin mulkin da aka yi a wannan kasar" a cewar Sheik Bala Lau.
Ya kara da cewa Shugabanin kasashen nan biyu suna darajanta Malaman addinai, abin da ke nuni da alamomin nasarar da ke tattare da yunkurin da aka sa gaba. Saboda haka ya ce malamai za su ci gaba da addu’a domin neman mafita a wajen ubangiji.
Wasu daga cikin Malaman Addinin Islama da suka kai ziyarar sulhu Nijar
"Kawo yanzu ana iya cewa Alhamdulillah addu’oin da ake yi sun sami karbuwa. Saboda haka lokaci ake jira kawai a ga komai ya warware cikin ruwan sanyi" a cewar Sheik Abdullahi Bala Lau Shugaban kungiyar Izalatul Bidi’ah wa Kimatus Sunnah na Najeriya, kuma shugaban tawagar Malaman Islama da ke shiga tsakani a dambarwar siyasar kasar jamhuriyar Nijar.
Saurari yadda hirar tasu ta kaya da Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5
Wata Tawagar Malaman Addinin Islama Ta Sake Kai Ziyarar Neman Sulhu Nijar .mp3