Wata kotun tarayya a nan Amurka zata takawa shugaban kasa birki wajen takaitawa kasashe shida masu yawan Musulmi zirga zirga

In this courtroom sketch, Muhanad Mahmoud Al Farekh, third from left, appears in federal court in New York April 2, 2015. Authorities say he traveled from Canada to Pakistan to train with al-Qaida, planning to kill American soldiers.

Wata kotun gwamnatin tarayya ta biyu ta kada kuriar taka birki kan amfani da ikonsa na shugaban kasa wajen takaitawa kasashe shida galibi Musulmi sukunin zirga zirga

Kotun daukaka kara ta tara dake San Francisco ta kada kuri’ar da ta sami goyon baya dari bisa dari jiya Litinin na kin amincewa da umarnin wucin gadin da shugaba Trump ya bayar, bisa hujjar cewa, shugaban kasar ya wuce gona da iri da ya bayar da umarni ranar biyu ga watan Maris, na “kare kasar daga ‘yan ta’adda da ke shiga Amurka”

Kwamitin da ya kunshi alkalai uku, yace yayinda dokar shige da fice da kare ‘yan kasa ta shekara ta dubu da dari tara da hamsin da biyu ta ba shugaban kasa iko kan shiga Amurka da kuma tabbatar da tsaron kasa, batun shige da fice, ko da na shugaban kasa ne, ba abu ne ya rataya a wuyan mutum day aba.

Hukumcin da kotun ta yanke jiya Litinin ya kara karfafa hukumcin da wata kotun daukaka kara ta hudu dake Virginia ta yanke, wadda ta goyi bayan hukumcin da wani alkali a jihar Maryland ya yanke na takawa wadansu bangarorin umarnin birki. Sai dai kotunan biyu sun bada hujjoji da suka sha banban.