Wata kotun gwamnatin tarayya ta samu dan tsohon shugaban kasar Guinea da matarsa da laifin bautar da wata yarinya wadda bata da takardar zama Amurka, da suka dauko daga kasarsu suka tilasa mata yin aiki a gidansu na tsawon shekaru goma sha shida ba tare da biyanta ba.
WASHINGTON DC —
An samu Mohamed Toure da Denise Cros-Toure, dukansu ‘yan shekaru hamsin da bakwai da haihuwa. Da laifin tilasawa yarinyar aiki da kuma boye bakuwar haure da hada baki a boye wadda bata da izinin zama Amurka. Sai dai an wanke mutanen dake zaune a birnin Dallas daga laifin hada baki su tilasawa wani aiki da ransa bai dauka ba.
Ba a riga an sa ranar da za a yanke masu hukumci ba. Sai dai zasu iya fuskantar daurin shekaru ishirin a gidan yari, bisa ga wata sanarwar, kuma tilas ne su biya ta diyya.
An kulle Toure da Cros-Toure ne bayanda aka same su da laifi ranar alhamis da yamma. Tun farko suna karkashin daurin talala tunda aka fara kamasu a watan Afrilu bara.
Lauyoyinsu sunce zasu daukaka kara.