Wata motar bas mai dauke da alhazan Shi'a daga Pakistan zuwa Iraqi ta yi hatsari a tsakiyar kasar Iran, inda akalla mutum 28 suka mutu, a cewar wani jami'i a ranar Laraba.
WASHINGTON, D. C. —
Hatsarin ya faru ne a daren Talata a Lardin Yazd da ke tsakiyar kasar Iran, in ji Mohammad Ali Malekzadeh, wani jami'in agajin gaggawa na kasar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na IRNA ya bayyana.
Hatsarin Bas a lardin Yazd
Ya kara da cewa wasu mutane 23 sun samu raunuka a hatsarin, kuma 14 daga cikinsu masu tsanani. Ya ce dukkan fasinjojin bas din sun fito ne daga Pakistan.
Akwai mutane 51 ne a cikin motar bas din a lokacin da hadarin ya afku a wajen birnin Taft mai tazarar kilomita 500 kudu maso gabashin Tehran babban birnin kasar Iran.
Iran
Hukumomi a Pakistan sun bayyana wadanda ke cikin motar bas din da cewa sun fito ne daga birnin Larkana da ke lardin Sindh na kudancin Pakistan.
-AP