Wasu Miskinan Bauchi Sun Dara Albarkacin Sallar Layya
Kayan abinci.
Wasu kungiyoyin agajin jin kai sun tuna da mabukata a jahar Bauchi
WASHINGTON, DC —
Kamar yadda akan yi shekara-shekara a lokutan salla, walau babba ko karama, a wannan karo ma a jahar Bauchi wasu kungiyoyin agajin jin kai da taimakon mabukata sun yi rabon nama da shinkafa da sauran kayayyakin abinci albarkacin sallar Layya.
Wakilin Sashen Hausa a Bauchi, Abdulwahab Mohamed ya halarci wurin rabon irin wadannan kayayyaki ya tattauna da masu rabawa da kuma wadanda aka baiwa:
Your browser doesn’t support HTML5
Ayyukan Jin Kai da Taimakon Mabukata a Jahar Bauchi - 2'51"
Mabukatan da aka rarrabawa shinkafa da nama da sauran kayan makulashe sun yi murna matuka, sannan suka yi godiya, tare da yin addu'ar Allah Ya maimaita.