Wata matashiya mai suna Onyinyechi Okegbulam, mai shekaru ashirin da biyu da haihuwa ta cimma ajalinta a sakamakon kin yarda da tayi ta auri saurayinta wanda ya biya mata kudin makaranta.
Mujallar ta wallafa cewar Okegbu 'yan kabilar Egbu daga karamar hukumar Owerri North ta jahar Imo, na tare da saurayinta ne da misalin karfe 7 na yamma kafin saurayin nata ya tattakura ya dirka mata harsashi a kai.
Wasu daga cikin shaidun a lamarin ya afku akan idan su, sun bayyana cewar saurayin ya harbe budurwar tasa ne a yayin da take tafiya zuwa wurin sa, sai da ya bari tazo kusa da shi sa'an nan ya harbe ta a kai.
Rahotanni sun nuna cewar da dai ya harbe ta, ya yi yunkurin daukar gawar ta ya saka a motar sa amma hakan bai sami yiyuwa ba a sakamakon wata mata da ta rafka ihu.
A cewar makwabtan iayaen marigayiyar, sun ce sun sami labarin cewar saurayin ne ya dauki dawainiyar biyan kudaden makarantar yarinyar, daga karshe kuma ta juya masa baya ta nuna cewar lallai ita wani daban zata aura. Sun kara da cewar sun ji labarin har an riga an sa mata rana da wani daban.
A halin da ake ciki yanzu dai jami'an tsaron 'yan sanda sun tabbatar da afkuwar lamarin kuma suna ci gaba da bincike.