Shugaba Donald Trump ya ba da umarnin dakatarwa da kuma yin nazari a kan wata doka, wace ta gindaya sharadin harkar kasuwancin Amurka a kasashen waje a tsawon shekaru hamsin, yana zargin cewa tsauraran matakan kauce ma bayar da cin hanci da rashawa ga jami'an kasashen waje da aka gindaya ma Amurkawa, na hana kasuwancin Amurka gogayya a kasuwannin duniya.
“(Jinkirta dokar) zai haifar da karin harkokin kasuwanci ga Amurka," a cewar Trump, yayin da ya sanya hannu a ranar Litini, kan umurnin sanya Ma’aikatar Shari’a ta dakatar da jerin binciken da ta keyi, sannan kuma ta yi nazarin Dokar Hana Aikata Rashin Gaskiya a Kasuwanci a Kasashen Waje, ta 1977 na tsawon watanni shida masu zuwa.
Umarnin na cewa "rashin daidaito da kuma saurin aiwatar da Dokar, wace ake kira FCPA a takaice, da ya shafi 'yan kasar Amurka da kamfanonin su– ta wajen Gwamnatin mu – kan al'adun kasuwanci na yau da kullum a wasu ƙasashe, ba kawai yana janyo barnata dan kayan aikin da ake da shi ba ne, wanda za a iya amfani da shi wajen mayar da hankali kan kiyaye 'yancin Amurka ba, har ma yana gurgunta Amurka wajen gogayyar tattalin arziki, wato kenan, har da tsaron kasa."