Trump Ya Ce Yana Da Ikon Korar Robert Mueller Dake Bincike Na Musamman

Robert Mueller, mai bincike na musamman akan zargin shishigin da Rasha ta yiwa zaben shekarar 2016

Biyo bayan samamen da aka kai gida da ofishin lauyansa a New York, a ci gaba da binciken zaben shekarar 2016 da ake yi, Shugaba Donald Trump ya ce yana da ikon korar mai binciken na musamman, Robert Mueller

Jiya Talata Fadar shugaban Amurka ta White House ta hakikance akan cewa, shugaban Amurka Donald Trump yana da ikon korar lauya na musaman da aka nada domin binciken alakar dake tsakanin yakin neman zaben shugaba Trump da shishigin da Rasha tayi a zaben shugaban kasar da aka yi.

Sarah Hukabee, jami’ar yada labarun shugaban tace an fada musu cewa shugaban yana da ikon daukan wannan mataki. Ms Hukabee ta yi wannan furuci ne, lokacinda yan jarida suka yi mata tambayar ko shugaba Trump yana da ikon korar Robert Mueller, lauya na musamman.

To amma masana harkokin shari’a da dama, sun ce idan ma shugaba zai dauki irin wannan mataki, tilas sai ya bi ta kan mukadashin atoni janaral Rod Rosenstein, wanda yana iya kin mutunta wannan umarni.

Wasu wakilan jam’iyar Democrat dana Republican a Majalisar dokoki sunce idan shugaban ya kuskura ya dauki wannan mataki, to hakan na iya cusa tsarin mulkin kasar cikin rikici.

Jiya Talata jaridar New York Times da ake bugawa a birnin New York ta buga labarin cewa shugaba Trump ya bukaci a kori Lauya Mueller a watan Disamban bara, kuma a dakatar da binciken da yake yi amma hakan bai yiwu ba.

Rahoton na jaridar New York Times ya ta’alaka ne akan hirarrakin da ya yi da wasu jami’an Fadar shugaban kasa ta White House.

Shi dai mukadashin atoni janaral Rod Roseinstein ya tsinci kansa cikin tsaka mai wuya, domin atoni janar Jeff Sessions ya tsame kansa daga binciken daya danganci shishigi ko kuma katsalandan Rasha a zaben shugaban Amurka.