Tattauna Hanyoyin Yaki da Talauci a Najeriya a Taron Kasa Zai fi Amfani
Nigeria National Assembly
Kungiyar hada kan arewacin Najeriya tace tattauna hanyoyin yaki da talauci a Najeriya a taron kasa zai fi amfani
WASHINGTON DC —
Kungiyar hada kan matasan arewacin Najeriya tace tattauna hanyoyin yaki da talauci a Najeriya, a taron kasa zai fi amfani ga al'umar Najeriya.
Shugaban, kungiyar Hassan Waziri Chinade ne ya furta haka a wata hira da yayi da wakilin Muryar Amurka, Nasiru Adamu El-Hikaya.
Yace yankin arewacin Najeriya, yafi sauran yankunan kasar yawan matasa, masu karancin ilimi da kuma karin talauci.
Wanda a cewarsa baida alfanu ga kasar, domin rashin ilimi da kuma talauci shike sa matasa fadawa aikata abubuwan da basu dace ba.
A wani labarin kuma Igwe Martins na yankin Ibo yayi watsi da masu dawo da kamfe din raba kasa ko kuma kafa kasar Biafra.