Taliban Ta Tabbatar Da Kashe 'Ya'yanta 21

'Yan Taliban

Kungiyar nan da doka ta haramtata a Pakistan ta Taliban, tabbatar da kashe mambobinta 21 a samame da wani jirgin Amurka mara matuki ya kai a makwabciya Afghanistan a ranar Laraba da ta gabata.

Harin da aka kai a gudnumar Kunar dake kan iyakar gabashin Afghanistan, ya auna sansanin horar da mayakan kungiyar nan da take kiran kanta Terik-e-Taliban ko kuma TTP a takaice, inda ake horar da masu kunar bakin wake, a cewar jami’an leken asirin Afghanistan da na Pakistan.

Jami’an sun ce galibin kwamandojin mayakan da kuma kwararrun masu bada horo a sansanin, suna cikin mutanen da aka kashe, wadanda suke shirin kaddamar da kai hare haren kunar bakin wake a Pakistan.

Kungiyar ta TTP ta fitar da wata sanarwa a jiay Juma’a, kuma ta tabbatar da kashe wani matashi dan kasa da shekaru 20, dan shugaban kungiyar, Mullah Fazullah kuma kungiyar ta sha alwashin daukar fansa a kan mummunar farmakin. Kungiyar 'yan ta’addan tace harin da jirgin Amurka mara matukin ya kai, ya taba makarantar addini kuma ya kashe daliban makaratantar da malamansu.