WASHINGTON, D.C. —
Wani dan Sandan rundunar 'yan Sandan jahar Ondo mai suna Mr. Israel Omowa, ya gamu da ajalinsa a hannun matar sa Mrs.Wumi Omowa, ita dai matar ta daba masa wuka ne a wuyar.
Hakan ya faru ne bayan da wata 'yar takaddama ta shiga tsakanin miji da matar a gidan su dake Olu, kan babban titin zuwa Ilesa dake garin Akure.
Kakakin rundunar 'yan Sandan jahar ta Ondo, Mr. Femi Joseph, ya tabbatar da afkuwar lamarin, ya kuma yi bayanai cewa matar ne ta kai mijin nata zuwa asibiti bayan da ta tafka masa ta'asar, tuni dai hukumar 'yan Sandan suka kulle matar Mrs. Omowa.