Shugabar Kungiyar Bringa Back Our Girls Ta Yiwa Allah Godiya da Sako 'yan Chibok
Shugabannin kungiyar Bring Back Our Girls
Hajiya Aisha Yusuf shugabar kungiyar Bring Back Our Girls da suka shiga zaman dirshen tun lokacin da aka sace 'yan matan Chibok ta yiwa Allah godiya bisa ga sako 21 daga cikinsu da fatan sauran ma za'a sakosu.
WASHINGTON DC —
Hajiya Aisha tace sun yi farin ciki da labarin kamar su zuba ruwa kasa su sha saboda matukar murna.
Tace tun can farko su san gwamnati zata iya kwato 'yan matan kuma gashi hakan ya soma tabbatuwa. Tace idan Allah ya yadda sauran ma za'a dawo dasu.
Saboda sun an gwamnatin yanzu zata iya kwato yaran suka nace sai an kwatosu.
Shugabar kungiyar Bring Back Our Girls ta rungumi daya daga cikin iyayen yaran
Your browser doesn’t support HTML5
Shugabar Kungiyar Bringa Back Our Girls Ta Yiwa Allah Godiya da Sako 'yan Chibok -1' 42"