WASHINGTON, D.C - Mabiya tamanin da tara na Cocin Good News International da ke dajin Shakahola da ke gabashin Kenya sun mutu. Hukumomi sun gano gawarwaki 81 daga cikin kaburbura tun ranar Juma’a, yayin da aka samu wasu ‘yan kungiyar asiri takwas da ransu amma daga baya suka mutu.
Shugaban Wata Kungiyar Asiri A Kenya Ya Fadawa Mabiya Da Su Kashe Kansu Da Yunwa Kafin Karshen Duniya
Mutuwar dai ta kasance daya daga cikin mafi muni da ke da nasaba da kungiyoyin asiri a tarihin baya-bayan nan, kuma ana sa ran adadin zai karu, inda kungiyar agaji ta Red Cross ta Kenya ta ce sama da mutane 300 ne aka bayar da rahoton bacewar su.
Shugaban kungiyar 'yan asirin Paul Mackenzie ya shiga hannun 'yan sanda tun ranar 14 ga Afrilu, wanda ake tsare da shi tare da wasu mambobin kungiyar 14. Kafofin yada labaran Kenya sun ruwaito cewa yana kin cin abinci da shan ruwa.
Shugaban Wata Kungiyar Asiri A Kenya Ya Fadawa Mabiya Da Su Kashe Kansu Da Yunwa Kafin Karshen Duniya
Stephen Mwiti, wanda matarsa da ’ya’yansa shida suka shiga kungiyar asiri kuma ake fargabar sun mutu, ya ce: “Ya ce shugaban ya gaya musu cewa su kashe kansu da yunwa kafin karshen duniya a ranar 15 ga Afrilu, yana mai cewa zai zama na karshe kuma zai kulle kofa.
Mwiti ya ce ya ji haka ne daga bakin wani tsohon ‘dan kungiyar asiri da aka kore shi saboda shan ruwa a lokacin azumin.
Shugaban Wata Kungiyar Asiri A Kenya Ya Fadawa Mabiya Da Su Kashe Kansu Da Yunwa Kafin Karshen Duniya
Ma’aikatan asibiti a garin Malindi da ke gabar teku, inda ake kai gawarwaki da wadanda suka tsira, sun ce sun ji irin wannan labari daga wadanda suka tsira.
Mwiti ya ce ya nuna damuwarsa ga 'yan sanda, amma yana jin an yi watsi da shi. Wata mai magana da yawun ‘yan sandan ta ce za ta amsa bukatar sauraransa daga baya ne.
Shugaban Wata Kungiyar Asiri A Kenya Ya Fadawa Mabiya Da Su Kashe Kansu Da Yunwa Kafin Karshen Duniya
Kamfanin dillancin labaran reuters ya kasa samun wani lauya ko wakilin da zai iya magana a madadin Mackenzie dangane da tuhumar da ake masa.
-Reuters