Shugaban da mai dakinsa sun nuna farin ciki da alfaharinsu kan nasarorin da Oshoala ta samu, da fatan zata cigaba da samo wasu dimbin nasarorin nan gaba.
Abuja, Nigeria —
Shugaba Tinubu da uwargidan sa Remi Tinubu sun karbi bakuncin gwarzuwar ‘yar wasan kwallon kafa ta mata a nahiyar Afirka, Asisat Oshoala a gidan shugaban kasa da ke Legas.
Tinubu da Mai Dakinsa Remi Tinubu na ganawa da Asisat Oshoala a Fadan Shugaban Kasa
Shugaban da mai dakinsa sun nuna farin ciki da alfaharinsu kan nasarorin da Oshoala ta samu, da fatan zata cigaba da samo wasu dimbin nasarorin nan gaba.
Shugaba Tinubu da Mai Dakinsa Remi Tinubu da Asisat Oshoala
Oshoala wada ta ke buga ma kungiyar wasan kwallon kafa na Barcelona a kasar Spaniya tamaula ita ce ta lashe kyautar gwarzuwar kwallon kafa ta Afirka ta 2023.
Remi Tinubu da Asisat Oshoala