Shugaban kasar Sudan ta Kudu, Silva Kiir, yayi barazanar cewa shi da kansa zaiyi jagorancin mayakansa suje su abkawa kungiyoyin tsageru dake tsakiyar kasar idan basu daina kai hare-hare akan fararen hular kasar ba.
WASHINGTON, DC —
A jiya ne shugaban yake cewa zai shiga gaba, soja su bi baya don suje Kogin Yei, su ja daga da wadanan ‘yan tsageran dake yawan kai hare-haren akan fararen hulan dake shigewa ta kan titunan dake kusa da kogin.
Ko a cikin makon jiya su ma jami’an MDD sun la’anci wadanan hare-haren da ake kaiwa a wannan yankin, wadanda ake jin watakila suna da alaka da kabilanci a tsakanin al’umman wurin.