Shawarwari Ga Samari Da 'Yan Mata Daga Malama Salma Yusuf

A shikin shirin samartaka na wanna makon ya sami ziyarar Uwa Kuma Jagora mai suna malama Salma Yusuf, wadda ta yi kira da bada shawarwari masu matukar ma'ana da anfani ga iyaye, shugabanni da kuma samari da 'yan mata dangane da irin yaudarar da ke tsakanin wasu samari da 'yan mata.

Da farko ta fara da cewa lallai yaudara aikin shedan ce, kuma ya kamata samari da 'yan mata su sani cewa duk wanda ya yaudari wani shima sai an yaudare shi ko yau ko gobe.

Ta kara da cewa akwai lokuta da dama da wasu samari ko 'yan mata kan sami kansu cikin wani mawuyacin hali wanda sanadiyyar yaudara ce ke tsunduma su cikin sa.

daga karshe ta bada shawarwari masu kyau ga matasa samari da 'yan mata musamman ta yadda za su kaucewa matsalar yaudara, ta kuma ba da shawara ga iyaye da su saka ido akan irin harkokin da 'ya 'yan su ke yi da irin abokan huldar su da kuma samarin su ko 'yan matan su.

Saurari cikakken bayanin a nan;