Shagulgulan Marbatar Sabuwar Shekarar 2019 a Wasu Biranen Duniya

Yadda aka yi wasannin wuta a birnin Hong Kong, Jan. 1, 2019.

An yi ta shagulgulan wasannin wuta a sassan duniya wadanda suka haskaka birane da dama a ranar Talata yayin da aka marabci shigowar sabuwar shekarar ta 2019.

Dubun dubatar mutane sun taru a fitaccen dadanlin nan na Time Square da ke birnin New York a nan Amurka, inda aka saki wata makekiyar kwallo, inda har ila yau a wannan karon, salon jefo kwallon ya yi nuni da muhimmancin ‘yancin walwalar ‘yan jarida da fadin albarkacin baki.

Sannan a karon farko, ‘yan sanda sun yi amfani da kananan jirage mara matuka, wadanda ke dauke da na’urorin daukan hoto 1,200, domin sa ido akan jama’a a birnin na New York.

A can birnin Paris da ke Farasansa kuwa, masu marabtar sabuwar shekarar sun taro a dandalin Champs-Elysees domin kallon wasannin wuta, duk da ci gaba da ake yi da yi wa gwamnatin Emmanuel Macron bore.

A birnin London, an ji kadawar makeken agogon nan ne da ake kira Big Ben da tsakar dare, duk da cewa ana yi wa shahararren agogon gyaran fuska.